Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dage kidayar 2023 na yawan mutane da gidaje da aka shirya fara yi a ranar 3 ga watan Mayun 2023.
Wannan na zuwa ne bayan wafa ganawa da shugaban ya yi da wasu mambobin majalisar zartaswar kasa, da shugaban hukumar kidaya ta kasa a fadar shugaban kasa a ranar Juma’a.
- Gwamnatin Jigawa Ta Dage Komawa Makaranta Saboda Kidayar Jama’a
- ‘Yansanda Sun Kama Direban Mota Da A-47 Guda 4 A Kano
A zaman, sun jaddada bukatar da ke akwai na yin kidayar jama’a da gidaje tun bayan wadda aka yi shekaru 17 da suka gabata domin tattara bayanai da za a yi amfani da su wajen fitar da tsare-tsaren da za su taimaka wa ci gaban kasa da kyautata rayuwar al’ummar Nijeriya.
A wata sanarwar da ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya fitar a ranar Asabar, Buhari ya yaba da irin tsare-tsaren da aka yi domin gudanar da kidayar ta 2023.
Kazalika, ya jinjina wa hukumar bisa fito da hanyoyi masu kyau da inganci da zai bayar da dama a gudanar da hakikanin kidaya kuma wanda za a amince da shi, musamman ta fuskar fito da na’urorin zamani da za su bayar da dama a gudanar da aikin kidayar bisa inganci.
Buhari daga bisani ya nemi hukumar da cewa su ci gaba da tsare-tsaren nasu ta yadda zai taimaka wa gwamnati mai zuwa ta dora daga inda aka tsaya don ganin an gudanar da kidayar kamar yadda aka tsara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp