Hukumar kula da tsarin fansho ta kasa (PTAD) ta sanar da fara aiwatar da karin kudaden fansho da aka amince da shi kwanan nan ba jimawa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, hukumar ta ce, karin ₦32,000, ga masu karɓar fansho da suka cancanta, an tabbatar da shi ne a cikin tsarin biyan fansho na watan Satumba na 2025.
- Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang
- Gwamnatin Tarayya Ta Soke Bikin Faretin Ranar Samun ’Yancin Kai
A cewar PTAD, ci gaban ya biyo bayan fitar da wani ɓangare na naira miliyan 420.188 daga cikin kuɗaɗen gaggawa na Naira biliyan 45 da shugaba Bola Tinubu ya amince da shi a baya.
“Wannan muhimmin al’amari ya sake tabbatar da himmar Gwamnatin Tarayya a fili don kiyaye walwala da haƙƙin ’yan fansho dake ƙarƙashin shirin (DBS) bisa ga manufar sabunta fata,” in ji Daraktan PTAD.
Mahukunta PTAD sun nuna jin daɗinsu ga shugaba Tinubu kan amincewa da tallafin gaggawar, wanda a cewarsu hakan zai inganta jin daɗi da walwalar masu karɓar fanshon.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp