Gwamnatin tarayya ta ce tana shirin sanya dokar hana yin Okada wanda akafi sani da Acaba.
Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ne yayi wata magana mai kama da jurwaye da kamar wanka a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar Shugaban kasa bayan kammala taron Majalisar Tsaro ta Kasa (NSC) da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.
Ya ce bincike ya nuna cewa ana amfani da okada wajen ayyukan hakar ma’adinai a fadin kasar nan. Hana hawa baburan ka iya katse hanyoyin da ‘yan ta’addan ke bi wajen samun kudade da kuma amsar kudin fansar wadanda su kayi garkuwa da su.
Ministan wanda ke tare da takwarorinsa na harkokin tsaron cikin gida, Rauf Aregbesola da Mohammed Dingyadi, ya ce taron ya mayar da hankali ne kan dabarun da ‘yan ta’addan ke amfani da su, sannan kuma ya za muyi wajen dakile muggan ayyukan nasu.
Ya ce akwai bukatar gwamnati ta dauki matakin haramta hawa babura saboda ‘yan ta’adda sun yi kaura daga hanyoyin da suka saba bi na samun kudaden gudanar da ayyukansu zuwa hakar ma’adinai da karbar kudin fansar Mutane ta Hanyar amfani da baburan.