Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan abubuwan cikin gida, Sanata Joel Onowakpo Thomas, ya sake tabbatar da kudurin Shugaban kasa Bola Tinubu na bunkasa karfin sashin fetur da iskar gas na cikin gida da sauran bangarorin a matsayin tabbataccen hanyar samar da ayyukan yi.
Ya yi wannan jawabi ne bayan ziyarar sa ido kan cibiyoyi da wuraren ayyukan hukumar bunkasa abun ciki ta Nijeriya (NCDMB) a Jihar Bayelsa.
- Gwamnatin Tarayya Ta Dukufa Wajen Karya Farashin Kayan Abinci – Minista
- Ƴansanda Sun Kama Shahararren Ɗan Damfarar Yanar Gizo A Bauchi
Ya ce, “Bari in ce ba za a iya kiyasin amfanin abubuwan da ake sarrafawa na cikin gida ba. Hakan zai haifar da samar da ayyukan yi ga jama’armu, bunkasa kadarori da fasaha masu muhimmanci, bunkasa kasuwancin cikin gida, inganta daidaiton biyan kudi da rage dogaro ga ayyukan kayayyakin kasashen waje da sauran nasarori masu yawa.”
Ya ce domin cimma wannan nasarar, akwai bukatar kara kyautata aikin hadin guiwa a tsakanin kwamitin majalisar da kuma hukumar NCDMB domin tabbatar da dokokin da suke akwai ana amfani da su yadda ya kamata.
“Kwamitin ba wai kawai zai tabbatar da sa ido ba ne, har ma zai tallafa wa hukumar a kokarin samar da da aiwatar da manufofin da ke inganta ci gaban abubuwan cikin gida, baya ga hadin gwiwarmu da hukumar, za mu hada kai da sauran masu ruwa da tsaki tare da samar da yanayin da zai samar da ci gaba ga harkokin kasuwanci na cikin gida da inganta samar da ayyukan yi.”
Ya yabawa hukumar bisa yadda ta aiwatar da dokar da ta ba da damar, ‘Dokar Ci Gaban Man Fetur da Gas ta Nijeriya (NOGICD) ta 2010.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp