Gwamnatin tarayya za ta fara aiwatar da shirin ‘Pulaku’, wani gagarumin shiri na samar da wuraren zama da nufin magance matsalolin rikicin manoma da makiyaya da kuma samar da hadin kan kasa.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, a ranar Talata, ya kaddamar da kwamitin gudanarwa da zai gudanar da aikin aiwatar da shirin domin cika alkawarin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na inganta rayuwar ‘yan Nijeriya baki daya.
- Gwamnonin PDP Sun Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Magance Matsalar Taɓarɓarewar Tattalin Arziki
- Mata Mu Kara Hakuri A Zamantakewar Aure -Aisha Seyoji
Kwamitin wanda ministan gidaje da raya birane Arc. Ahmed Musa Dangiwa zai jagoranta, yana da wakilan gwamnonin jihohin da abin ya shafa a matsayin mambobi.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da ministan noma da samar da abinci, Sen. Abubakar Kyari; wakilan Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Darakta Janar na Hukumar Bayar da Tallafin Jama’a (BPP), rukunin BUA, rukunin Dangote da Darakta Janar na NEMA da dai sauransu.
Da yake jawabi yayin kaddamar da kwamitin aiwatarwar a fadar shugaban kasa da ke Abuja, mataimakin shugaban kasar a wata sanarwa da kakakinsa Stanley Nkwocha ya fitar, ya ce dole ne a dauki aikin a matsayin gaggawa domin tunkarar kalubalen da ke barazana ga ci gaban Nijeriya.