Hukumar da ke kula da wutar lantarki ta Nijeriya (NERC) ta amince da karin farashin mitar wutar lantarki da ake biya a kasar.
A wata takardar da shugabannin NERC, Sanusi Garba da Dafe Akpeneye suka sanyawa hannu kuma mai kwanan wata 5 ga watan Satumba, 2023, ta bayyana cewa, mita mai layi daya za a biya Naira N81,975.16 maimakon Naira N58,661.69 da ake biya a baya, sai kuma mita mai layi Uku, za a biya Naira N143,836.10 maimakon Naira N109,684.10
Takardar ta ce, an sabunta farashin ne don tabbatar da daidaiton farashin mitoci ga masu amfani da wutar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp