Ma’aikatar lafiya da jin dadin jama’a ta tarayya, ta mika sabbin cibiyoyin kula da mata da yara (MCC) guda 14 da aka gina ga asibitocin koyarwa na gwamnatin tarayya da cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya (FMC) domin gudanarwa.
Dakta Tunji Alausa, karamin ministan lafiya da walwalar jama’a ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja ranar Laraba.
- Gwamnati Ta Rufe Kwalejin Kiwon Lafiya 8 A Adamawa
- ‘Yansanda Sun Kama Dan Bindiga, Sun Ki Karbar Cin Hancin Miliyan 8 A Taraba
A cewarsa, matakin na daga cikin kokarin yaki da yawan mace-macen mata da kananan yara a Nijeriya.
Alausa ya ce, cibiyoyin sun hada da cibiyoyi shida masu dauke da gadaje 80 da kuma MCC guda takwas masu gadaje 100 a jihohi 12.
Jihohin da suka samu wannan rabo sun hada da Bauchi, Delta, Filato, Taraba, Abia, Kuros Riba, Oyo, Kebbi, Ondo, Kano, Benue, da Ogun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp