• English
  • Business News
Sunday, July 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Soke Faretin Ranar Dimokuraɗiyya, Tinubu Zai Yi Wa ‘Yan Ƙasa Jawabi 

by Naziru Adam Ibrahim
2 months ago
in Manyan Labarai
0
Irin Ministocin Da ‘Yan Nijeriya Ke Tsammani Daga Gwamnatin Tinubu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnatin Tarayya ta soke faretin soja da aka saba yi a duk zagayowar ranar dimokuraɗiyya, wanda za a yi a gobe Alhamis, 12 ga watan Yuni, 2025, don bikin cikar Nijeriya shekaru 26 na dawowa mulkin dimokuraɗiyya.

Kwamitin Shirya Bikin Ranar Dimokuraɗiyyar ne, ya shaida haka yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar ƙasa kai-tsaye da misalin ƙarfe 7 na safe a ranar Alhamis, ba tare da faretin soja kamar yadda aka saba a baya ba, kan zai halarci zama na musamman na Majalisar Tarayya da misalin ƙarfe 12 na rana.

  • A Bai Wa Kudu Tikitin Takara A 2027 Ko PDP Ta Ruguje – Wani Jigo A PDP
  • Nijeriya Ta Fuskanci Cikas Wajen Karɓo Rancen Dala Biliyan 5 Daga Saudiyya

Yayin zaman, ana sa ran zai gabatar da jawabai kan halin da ƙasar nan ke ciki tare da nazari kan yadda dimokuraɗiyyar Nijeriya ke gudana, da kuma kira na musamman don haɗin kai wajen sake fasalin tsarin ƙasa.

Hakazalika, a yammacin ranar da misalin ƙarfe 4, za a gudanar da babban taron jawabi a Dandalin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda za a tattauna kan ci gaban dimokuraɗiyya mai taken: “Ƙarfafa Nasarorin Dimokuraɗiyyar Nijeriya: Muhimmancin Sauye-sauyen Da Za Su Dore.”

An buƙaci jama’ar ƙasar nan da su saurari jawabin shugaban ƙasa da kuma bayar da tasu gudunmawar cikin tattaunawar kan yadda za a zurfafa ginshikan dimokuraɗiyya da sauye-sauye masu ma’ana.

Labarai Masu Nasaba

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: JawabiRanar DimokuraɗiyyaTinubu
ShareTweetSendShare
Previous Post

Tsohon Ɗalibi Ya Kai Hari Makarantarsu A Austria, Ya Kashe Ɗalibai 9

Next Post

Guguwa Za Ta Sa Kasashen Sin Da Afirka Su Kara Rike Hannayen Juna

Related

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 
Wasanni

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

13 hours ago
Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson
Siyasa

Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson

18 hours ago
An Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
Manyan Labarai

An Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja

19 hours ago
Gwamnatin Kano Ta Gabatar Da Buƙatu 10 A Gaban Kwamitin Gyaran Tsarin Mulkin Nijeriya
Da ɗumi-ɗuminsa

Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Bincikar Kwamishinan Sufuri Kan Karɓar Belin Dilan Ƙwaya A Kano

1 day ago
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12
Manyan Labarai

Dangote Ya Ajiye Muƙamin Shugabancin Kamfaninsa Na Siminti

2 days ago
Ganawar Tinubu Da Kwankwaso Alkairi Ce – Mataimakin Shugaban FUDMA
Manyan Labarai

Tinubu Na Yi Wa Arewa Manyan Ayyuka – Martanin Fadar Shugaban Ƙasa Ga Kwankwaso 

2 days ago
Next Post
Guguwa Za Ta Sa Kasashen Sin Da Afirka Su Kara Rike Hannayen Juna

Guguwa Za Ta Sa Kasashen Sin Da Afirka Su Kara Rike Hannayen Juna

LABARAI MASU NASABA

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

July 27, 2025
Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 6 A Kaduna Da Zamfara

Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 6 A Kaduna Da Zamfara

July 27, 2025
aure

Ko Kin San… Matsalolin Mahaifa Da Suke Hana Haihuwa 

July 27, 2025
VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

July 27, 2025
Yadda Ake Faten Acca

Yadda Ake Faten Acca

July 27, 2025
Hanyoyin Gyaran Gashi

Hanyoyin Gyaran Gashi

July 27, 2025
Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

July 26, 2025
Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

July 26, 2025
Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

July 26, 2025
Kasar Sin Na Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantu A Gaza Tare Da Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta

Isra’ila Na Sanya Alamar Rusau A Dubban Gidajen Fararen Hula A Gaza

July 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.