• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Fatali Da Zargin Da Obi Ya Yi Mata Kan Karin Kasafin Kuɗi

by Sulaiman
2 years ago
Tinubu

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce karin kasafin kuɗi na shekarar 2023 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba wa hannu a ranar Laraba, 8 ga Nuwamba, 2023 ba a yi shi cikin rashin tunani da hangen nesa ba, an yi shi ne bisa la’akari da halin matsin tattalin arziki wanda Nijeriya ta ke fuskanta a yanzu. 

A wata takarda ga manema labarai da ya rattaba wa hannu a ranar Alhamis, hadimin ministan na musamman a ɓangaren yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim, ya ruwaito cewa ministan ya yi kira ga ɗan takarar zama shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour a zaɓen 2023 da ya samu lokaci ya zauna ya karanta kundin karin kasafin kuɗin na naira tiriliyan 2.17 a tsanake domin ya fahimce shi da kyau, zai ga ya ƙunshi tanadin kuɗin da aka yi wa muhimman ayyuka irin su tsaro, aikin gona, wadata ƙasa da abinci, ayyuka da gidaje, ƙarin albashi ga ma’aikata, shirin bada rance ga ɗalibai, da hanyoyin sauƙaƙa wa talaka halin da ya ke ciki, da sauran su, waɗanda an yi su ne don a ƙarfafa ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar tare da inganta halin zamantakewa a tsakanin ‘yan Nijeriya.

  • Tinubu Ya Rattaba Hannu A Kan Karin Kasafin Kudi Na Naira tiriliyan 2.17 Na Shekarar 2023.
  • Ka Nemi Sana’a Siyasa Ba Taka Ba Ce,Tinubu Ga Peter Obi

Ya ce: “Ɗimbin tanade-tanaden da ke cikin ɗorin kasafin kuɗin ya nuna babban burin Shugaba Tinubu da yadda ya ke matuƙar son ya tallafa wa ayyukan da gwamnati ta sa a gaba, ya tunkari matsalar tsaro gaba-gaɗi, kuma ya gaggauta haɓaka hanyoyin da za a bi a magance matsalolin ƙasar waɗanda cire tallafin mai ya haifar.

Idris ya yi kira ga ‘yan siyasar adawa da su kasance masu sani kuma adalai wajen bayyana ra’ayin su mabambanta, sannan su kauce wa yi wa gaskiya jirwaye don kurum su cimma burin siyasa.

LABARAI MASU NASABA

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

Ya yi bayanin cewa an yi ɗorin kasafin kuɗin ne bayan tattaunawa tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki da su ka dace waɗanda su ka bada tabbacin cewa kasafin ya yi daidai da buƙata da muradun jama’ar Nijeriya.

Idris ya nanata cewa kamar yadda Shugaba Tinubu ya ke da son ganin an bi dukkan ƙa’idoji wajen sarrafa kuɗin gwamnati, to sai da aka yi nazari a tsanake kan kowane lissafi a kasafin kuɗin don tabbatar da cewa an kashe kuɗaɗen jama’a a yadda ya kamata.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce
Manyan Labarai

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Labarai

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

October 25, 2025
Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu
Manyan Labarai

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

October 25, 2025
Next Post
Mutuwar farad-daya

Yawaitar Mutuwar Farad-daya A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

October 25, 2025
Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

October 25, 2025
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025

October 25, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.