Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, wacce ta yi wannan gargadin a madadin gwamnatin tarayya, ta yi gargadin cewa dole ne a dauki matakan da suka dace a cikin al’ummomin da abin ya shafa. Sanarwar da Ma’aikatar Muhalli ta fitar ta ce, biyo bayan hasashen da ta yi na samun ruwan sama mai karfi a jihohin, za a iya samun ambaliyar ruwa tsakanin 10 ga Agusta zuwa 14 ga Agusta, 2025.
Ma’aikatar ta yi wannan gargadin ne ta cibiyar gargadin ambaliya ta kasa (FEW), a wata takardar da Daraktanta na Sashen Kula da zaizayar kasa da ambaliyar ruwa, Malam Usman Abdullahi Bokani, ya sanyawa hannu jiya a Abuja, ta kuma yi hasashen cewa jihohin da ta yi hasashen hakan sun hada da Adamawa, Bauchi, Nasarawa, Kaduna, Katsina da Kebbi.
- Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu
- Fa’ida Da Muhimmancin Tattalin Lokaci Ga Ɗan’adam
Har ila yau akwai, Jihohin Kano, Neja, Taraba, Jigawa, Yobe, Zamfara, Sokoto, Borno, da Kwara.
Sanarwar ta zayyana wasu fitattun garuruwa da al’ummomin da ka iya fuskantar mummunar ambaliyar ruwa da suka hada da Jimeta, Mubi, Keffi, Kafanchan, Birnin Kebbi, Minna, Gusau da Sakkwato.
A cikin jihohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa da aka fi tsammanin ambaliyar za ta yi kamari, ga su guda 10 kamar yadda ta bayyana: Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, da Birnin Kebbi.
Bokani ya bukaci mazauna yankin da hukumomin jihar da su dauki matakan kare rayuka da dukiyoyi cikin gaggawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp