Gwamnatin Tarayya ta ce za ta dauki ‘yan sintiri aiki don samar da tsaro a hanyoyin layukan dogo da ke a daukacin fadin kasar nan.
Biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris 2022, gwamnatin ta dauki sabbin gabaran samar da tsaro domin jiragen kasan su ci gaba da gudanar da safarar matafiya a cikin nasara.
- Yadda Wasu Mata 2 Suka Haifi Jarirai Shida-Shida A Yobe
- ‘Yan Sintiri Sun Kashe ‘Yan Bindiga 12 A Jihar Taraba
Mai bai wa Ministan sufurin jiragen kasa shawara ta musamman, Odukale Oluwafemi ne ya sanar da hakan a wani taro da kungiyar matasa ta (NYC) ta shirya a garin Abuja.
Ya ce, shugaba Muhammadu Buhari har yanzu, bai samun yin barci mai dadi biyo bayan harin na jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, inda ya kara da cewa, ma’aikatar suufurin jiragen kasa na yin aiki kafa da kafa da jami’an tsaro don a tabbatar da an bai wa fasinjojin da kuma kayansu kariyar da ta dace idan jiragen sun dawo su fara gudanar da aiki.
A cewar Oluwafemi, shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin iya kokarinsa wajen samar da wadataccen tsaro a kasar nan, inda ya kara da cewa, ita ma ma’aikatar ta sufurinjiiragen kasa, na ci gaba da yin na ta kokari wajen bai wa fasinjojin tsaron da ya kamata.
Ya ce “A yanzu na san mutanen na cikin fara shirin yin tafiye-tafiye don zuwa garuruwansu yin bikin sabuwar shekara, don haka, ma’aikatar sufurin jiragen kasa za ta yi iya kokarinta wajen ganin jiragen agen, musamman sun dawo don ci gaba da bin hanyar Abuja zuwa Kaduna.