Gwamnatin tarayya na shirin kara gina madatsun ruwa (Dam) domin tabbatar da samun wadataccen ruwan sha da kuma ayyukan noman rani a fadin kasar nan.
Babban Darakta na Hukumar raya Kogin Neja (LNRBDA), Dakta Adeniyi Saheed Aremu ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, Ilorin jihar Kwara.
- Rundunar Sojin Sama Ta Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama Tare Da Lalata Maboyarsu A Katsina Da Zamfara
- Xi Ya Jaddada Zurfafa Gyare-gyare Don Inganta Kwarewa A Sabbin Fannoni
Dakta Aremu ya bayyana hakan ne a wajen taron kungiyar ‘yan jaridu ta kasa (NUJ) reshen jihar Kwara kan harkokin majalisar jihar karo na 42 da ya gudana a babban birnin jihar, Ilorin.
A wajen taron, Aremu ya ce, kudurin gina karin madatsun ruwa ya yi daidai da abubuwan da gwamnatin Bola Tinubu ke jagoranta.
Ya yi nuni da cewa, idan aka gina madatsun ruwan, za su amfanar matuka musamman ga bangare harkokin noman rani.