A jiya ne Majalisar Zartarwa ta Tarayya FEC, ta amince da kashe Naira biliyan N24.20 a wasu kwangiloli biyu domin samar da intanet kyauta a wuraren taruwar jama’a 75 da suka hada da filayen tashi da saukar jiragen sama guda, manyan makarantu da kasuwanni guda 20 a fadin kasar nan domin tallafa wa kanana da matsakaitan masana’antu.
Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Ali Pantami, ya ce hukumar sadarwa ta Nijeriya ce (NCC) za ta gudanar da ayyukan.
Ya ce an zabo wurare mafi karanci Uku daga cikin shiyyoyi shida da muke da su a siyasa.
Ya ce, “A Kudu maso Yamma, akwai Jihar Legas da Ondo; Kudu maso Gabas, Akwai jihar Imo, Anambra da Enugu; Kudu maso Kudu, akwai jihar Fatakwal da Akwa Ibom; Arewa ta Tsakiya, Akwai Abuja da birnin Ilorin; Arewa maso Yamma, akwai Jihar Kano, Sokoto da Kebbi; Arewa maso Gabas, akwai birnin Yola, Maiduguri da Gombe.
“Za a kammala aikin a mafi karancin lokaci, watanni hudu, mafi tsawo watanni biyar kuma akwai tanadin kudaden da ake bukata.”
Pantami ya ce gwamnati mai ci ce ta tara kudaden da za a gudanar da ayyukan da su.