Gwamnatin Tarayya da hadin gwiwar Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund), za ta samar da cibiyoyi fiye da 24 na fasaha da kirkire-kirkire a fadin Nijeriya don baiwa ‘yan Nijeriya damar bunkasa sana’o’insu.
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a Abuja, lokacin da ya kai ziyara cibiyar Innov8 Hub, tare da masu ruwa da tsaki ciki har da babban sakatare na TETfund, Arch. Sonny Echono.
- Mazauna Yankunan Karkarar Sin Sun Samu Karin Kyautatuwar Rayuwa
- Gwamnatin Jigawa Za Ta Raba Kayan Abinci Don Rage Raɗaɗin Tsadar Kaya Da Azumi
Innov8 cibiya ce mai horar da matasa fannin kirkire-kirkire da Fasahohi.
Mammam ya ce shirin samar da cibiyoyin fasaha fiye da 24 a fadin kasar nan, an yi shi ne don baiwa matasa ‘yan Nijeriya damar samun sana’o’i da fasahohi a bangarori daban-daban.