• English
  • Business News
Wednesday, October 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Yekuwar Rigakafin Cutar Ƙyandar Jamus

by Sulaiman
5 months ago
Kyanda

Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin tallafa wa kamfen na ƙasa da za a gudanar don yi wa yara rigakafi daga cututtukan ƙyandar jamus (wato measles-rubella), wanda ake shirin farawa a watan Oktoba na bana.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a yayin da tawagar Cibiyar Kula da Lafiya da Hanyoyin Magance Matsalolin Abinci (C-WINS) ta kai masa ziyarar ban-girma a ofishin sa a ranar Talata.

  • Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 2 Sun Sace 2 A Wurin Haƙar Ma’adanai
  • An Kashe Wani, Wasu Sun Jikkata A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Neja

Ministan ya yaba da ƙoƙarin ƙungiyar wajen kula da lafiyar jama’a da kare lafiyar yara, yana mai tabbatar da cewa ma’aikatar sa za ta mara baya wajen faɗakar da jama’a domin tabbatar da nasarar wannan yekuwar.

Ya ce: “Kun zo inda ya dace. Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai tana aikin ta ne don tallafawa da kuma bunƙasa irin waɗannan shirye-shiryen.

“Za mu yi aiki tare da ku da hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar, ciki har da Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da kuma kafafen yaɗa labarai na gwamnati, domin tabbatar da cewa ’yan Nijeriya sun samu cikakken bayani game da haɗarin cutar ƙyandar jamus da kuma muhimmancin rigakafin.”

LABARAI MASU NASABA

Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo

Ministan ya bayyana gabatarwar da C-WINS ta yi a matsayin mai motsa zuciya kuma mai cike da ƙarin haske.

Ya ce: “A yau na koyi abubuwa da dama. Yawancin ’yan Nijeriya, kamar ni kai na, sun san cutar masassarar cizon sauro amma ba su san da ƙyandar jamus da mummunan tasirin ta ba.

“Gaskiya batun cewa za a iya haihuwar yara makafi, kurame ko kuma masu nakasar zuciya sakamakon kamuwa da ƙyanda daga uwa a lokacin ɗaukar ciki babbar masifa ce da ya kamata mu haɗa kai mu daƙile ta.”

Ya ƙara da cewa ma’aikatar za ta haɗa hannu da sauran hukumomin da suka dace wajen tsara saƙonnin faɗakarwa da shirye-shiryen ilimantar da al’umma.

Ya kuma shawarci tawagar da su nemi haɗin kan Majalisar Tarayya domin samun cikakken goyon baya na doka.

Ya ce: “Ba ma so wannan zama ya tsaya nan kawai. Mu mayar da wannan haɗin gwiwa abin da zai ɗore, mai amfani, kuma mai faɗi da tasiri. Rigakafi ya fi magani — kuma wannan fannin ne inda bayani ke ceton rayuka ainun.”

A cikin nata jawabin, jagorar tawagar C-WINS, Dakta Nihinlola Mabogunje, ta jaddada gaggawar wayar da kan jama’a kafin lokacin fara kamfen ɗin.

Ta gabatar da cikakken bayani kan muhimmancin rigakafin daga cututtukan ƙyandar jamus fata, musamman a matsayin da Nijeriya ke da shi wajen yawaitar waɗannan cututtuka.

Dakta Mabogunje ta bayyana cewa Nijeriya tana da kusan kashi 20 cikin ɗari na dukkan cututtukan ƙyandar da ake samu a duniya, inda yankin Arewa-maso-gabas yake ɗauke da fiye da kashi 60 cikin ɗari na waɗanda abin ya shafa a ƙasar nan.

Dangane da ƙyandar jamus, ta bayyana cewa cutar tana barazana musamman ga mata masu juna biyu, domin kamuwa da cutar a watannin farko na ɗaukar ciki yana iya janyo haihuwar jarirai masu nakasa kamar makanta, kurmancewa ko lalacewar zuciya.

Ta tabbatar da cewa rigakafin da za a yi amfani da shi yana da inganci kuma ba shi da wani haɗari ga lafiyar mutum, tana mai cewa tun tuni ake amfani da shi, fiye da shekaru 50 a duniya, kuma ya ceci rayuka sama da miliyan 94.

Ta kuma yaba da aikin Hukumar NAFDAC wajen tantancewa da amincewa da rigakafin domin amfani da shi a Nijeriya.

Ta roƙi Gwamnatin Tarayya da ta jagoranci faɗakarwar a matakin ƙasa domin kawar da ji-ta-ji-ta da ƙarfafa gwiwar jama’a.

Likita Mabogunje ta ce: “Don cimma burin kashi 95 na yawan masu karɓar rigakafi, muna buƙatar saƙonnin da suka dace, masu sahihanci da kuma daidaito, waɗanda za a isar ta hanyoyin da ’yan Nijeriya suke yawan dogaro da su a kullum.”

A martanin sa, Minista Idris ya umurci jami’an sashen sadarwa na ma’aikatar sa da su yi aiki tare da C-WINS domin ƙirƙirar kayan faɗakarwa da suka dace da al’adun jama’a, waɗanda za a yaɗa ta kafafen watsa labarai na gwamnati da masu zaman kan su a dukkan faɗin ƙasar nan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447
Labarai

Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

October 21, 2025
Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu
Labarai

Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo

October 21, 2025
Sabbin Ministoci
Labarai

Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni

October 21, 2025
Next Post
Hukumar kashe gobara

An Samu Asarar Dukiya ta Miliyan ₦273, Tare Da Mutuwar Mutum 5 A Kano - Hukuma

LABARAI MASU NASABA

Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

October 21, 2025
Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa

Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa

October 21, 2025
Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

October 21, 2025
Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

October 21, 2025
Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu

Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo

October 21, 2025
Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?

Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?

October 21, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni

October 21, 2025
Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin

Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin

October 21, 2025
Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan ₦2.3 Ga Tsofaffin Ma’aikata Da Iyalansu

Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi

October 21, 2025
Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia

Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia

October 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.