Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, wajen daukaka darajar taken kasar.
Goyon bayan gwamnatin tsakiya, na zuwa ne bayan da aka bayar da rahoton cewa, shafin matanbayi ba ya bata wato Google, ya ki sanya taken kasar Sin, a saman filin neman sakamakon kalmomin “Hong Kong” da “taken kasa” kamar yadda gwamnatin yankin musamman na Hong Kong ta bukata. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp