Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Idi Barde Gubana, ya bayyana cewa gwamnatin jihar na ƙoƙarin inganta tsaro a dukkanin faɗin jihar.
Hon. Gubana ya bayyana hakan ne yayin jagorantar taron tattaunawa da shugabannin tsaro a jihar, a yayin da ake shirin gudanar da taron ƙungiyar gwamnonin Arewa Masu Gabas a ƙarshen watan Afrilu.
- Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Ayyukan Sadarwa
- Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci Ta Yaba Wa Gwamna Lawal Kan Matakan Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
A yayin taron, Hon. Gubana ya bayyana cewa gwamnati tana aiki tare da jami’an tsaron sojoji, ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro mai ɗorewa a Jihar Yobe.
Ya ce, “Mun tattauna da shugabannin jami’an tsaro kan al’amuran tsaro, cikin shirye-shiryen gudanar da taron ƙungiyar gwamnonin Arewa Masu Gabas da zai gudana nan Damaturu.”
Kwamishinan ‘yansandan Jihar Yobe, Mista Emmanuel Ado, ya bayyana cewa kwamitin tsaron ya yi nazari mai kyau kan yanayin tsaro a jihar a cikin watan da ya gabata, inda aka ga ci gaba wajen tabbatar da zaman lafiya.
A nasa ɓangaren, mai bai wa Gwamnan Shawara Kan Al’ammuran Tsaro, Janar Dahiru Abdusalam (Mai Ritaya), ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar tana ɗaukar matakai tare da jami’an tsaro don samar da tsaro mai inganci.
Ya kuma bayyana cewa duk da matsalolin tsaro da ake fuskanta a hanyar Damaturu zuwa Gujba, jami’an tsaro na ƙoƙarin yin sintiri domin tabbatar da tsaro.
Janar Dahiru ya ce, “Koda yake muna fuskantar ƙalubale daga Boko Haram a yankunan wasu sansanin sojoji, jami’an tsaro na ci gaba da aikinsu domin kare yankin.”
Ya ƙara da cewa, “Muna taka-tsan-tsan musamman wajen daƙile karɓar haraji daga Boko Haram a wasu yankuna. Wannan al’amari yana da matuƙar wahala, amma muna fatan za mu samu nasara.”
Janar Dahiru ya tabbatar da cewa akwai tsaro a dukkanin sassan jihar tare da haɗin gwiwar sojoji, ‘yansanda, Civilian JTF da ‘yan sa-kai.
Ya kuma bayyana cewa za a fitar da sabbin dabaru cikin makonni masu zuwa domin yaƙar ‘yan ta’adda.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp