• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Zamfara Ta Ƙaryata Rahoton Karɓo Lamuni Da Wata Jarida Ta Yaɗa

by Sulaiman
4 months ago
Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ƙaryata zargin da ake na cewa Gwamna Lawal ya ciyo bashin kuɗi, inda ta bayyana irin waɗannan ikirari a matsayin wani mummunan hali na Sahara Reporters.

 

A ranar Litinin da ta gabata ne Sahara Reporters ta buga wani labari mai taken ‘RAHOTON MUSAMMAN: Takardun Kasafin Kuɗi Sun Fallasa Ikirarin Ƙarya Da Gwamnan Zamfara Lawal Ya Yi Na Rashin Karbar Lamuni — An Karbi Bashin Naira Biliyan 34 A Ƙarƙashin Gwamnatinsa’.

  • Al’ummun Afrika Da Sin Ba Za Su Taba Mantawa Da Gudunmuwar Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ba
  • Xi Jinping Zai Halarci Bikin Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan Da Yakin Kin Tafarkin Murdiya

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau, ya bayyana Sahara Reporters a matsayin kafar yaɗa labarai ta yanar gizo da ke jin daɗin yaɗa labaran ƙarya.

 

LABARAI MASU NASABA

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

Sanarwar ta ƙara da cewa, aikin Sahara ba wai kawai aikin jaridar bogi ba ne; ya samo asali ne zuwa da suna ‘Gonzo’, wanda ke da alaƙa da ƙarairayi wajen bayar da rahoto.

 

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An ja hankalinmu kan labaran ƙarya da Sahara Reporters ke yaɗawa, shafin da ya shahara wajen yaɗa labaran ƙarya domin tayar da ƙura a intanet.

 

“A yayin tattaunawa da manema labarai kai tsaye a makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana ƙudirinsa na ɗaukar nauyin kasafin kuɗi, inda ya tabbatar da cewa bai karbi lamuni na cikin gida ko na ƙasashen waje ba tsawon shekaru biyu da ya yi yana mulki.

 

“Amma abin ya ba mu mamaki, manyan jami’an yaɗa labaran ƙarya, Sahara Reporters, sun wallafa abin da suka sanya a matsayin wani rahoto na musamman na yadda aka karbi rancen Naira Biliyan 34 a ƙarƙashin kulawar Gwamna Lawal.

 

“Rahoton na Sahara ya bayyana ƙarara irin gazawar su wajen neman ƙwararan bayanai tare da yin nazari kan takardar kasafin kuɗin jihar Zamfara.

 

“Rahoton lamuni na naira biliyan 34 da Sahara Reporters ta yaɗa na buƙatar ƙarin haske domin tabbatar da cewa jama’a sun fahimci gaskiyar lamarin.

 

“An shirya Kasafin Kuɗi na 2023 ne a zamanin gwamnatin Bello Matawalle, wanda a yanzu shi ne Ƙaramin Ministan Tsaro, daga cikin kasafin kuɗin, an ware biliyan 53.2 domin kula da lamuni da gwamnatin jihar ta karbo.

 

“Duk da cewa ba a samu lamuni a wannan adadi na sama ba, gwamnatin jihar Zamfara ta kashe biliyan 34 wajen biyan kuɗin ruwa na rance daban-daban da gwamnatocin baya suka karba, hakan ya nuna yadda Dauda Lawal ya jajirce wajen rage yawan bashin da ake bin Zamfara da kuma hana karbar ƙarin lamuni.

 

“Duk dandali da ya ƙuduri aniyar yin aikin jarida na gaskiya zai gudanar da cikakken bincike don tabbatar da hasashensa da kuma tabbatar da sahihancin sa, amma Sahara Reporters ta zabi wata hanya ta daban, ta tsaya kan tsarin aikin jaridar bogi.

 

“Ya kamata Sahara Reporters ta tambayi tsohon Gwamna Bello Matawalle kan yadda ya yi amfani da lamunin da ya karba a zamaninsa, wanda hakan bai haifar da wani ci gaba ba, rancen da muke biya kenan.

 

“Gwamna Dauda Lawal bai karbi rance ba tsawon shekaru biyu da ya yi yana Gwamnan jihar Zamfara.

 

“Muna ƙalubalantar Sahara Reporters da su samar da duk wasu takardun da ke nuna gwamnatin Zamfara mai ci na neman lamuni, ko a cikin gida ko kuma a waje.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140
Labarai

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Majalisar Dattawa
Labarai

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa
Labarai

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Next Post
Sayar Da Makamai: Goyon Baya Ko Cin Riba?

Sayar Da Makamai: Goyon Baya Ko Cin Riba?

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.