Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bada hutun mako daya domin baiwa ma’aikatan gwamnati damar yin rijista da kuma amsar katin zabe na dindindin (PVCs).
Kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Gusau.
“Wannan tafito ne don sanar da jama’a cewa mai girma Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ayyana mako mai zuwa daga 20 zuwa 24 ga watan Yuni a matsayin makon hutun aiki.
“An yi Hakan ne don baiwa jama’a da ma’aikatan jihar damar zuwa yankunansu domin yin rijista da karbar katin zabe na dindindin (PVCs).”
A cewarsa, ana sa ran shugabannin al’umma za su tabbatar da cewa Jama’a masu kada kuri’a a duk fadin Jihar sun yi rajista tare da samun katin zaben su na dindindin (PVC).