Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta bayyana kammala shirin yi wa mata marayu aure da ke zaune a gidajen marayun jihar da ke Gusau.
Mataimakiya ta musamman kan yada labarai da sadarwa ta Uwargidan gwamnan, Zara’u Musau ce, ta bayyana hakan ga manema labarai a Gusau.
- Zulum Ya Bayar Da Umarni A Binciki Gawar ‘Yar Dan Majalisa Da Aka Kashe A Jihar Borno
- Tinubu Ya Kaddamar Da Shirin Raba Naira Tiriliyan N1.25 Ga Magidanta Miliyan 15
“A cewar Huriyya Dauda ta kai ziyara gidan marayun da ke Gusau, ta jadadda bayar da kulawa da tarbiyya da walwala ga marayu a jihar.
“Uwar marayun ta kara da cewa gwamnatin Zamfara, karkashin jagorancin maigidanta za ta yi iyaka kokarinta wajen sauke nauyin auren, da abubuwan da amare ke bukata ga iyaye da yardar Allah za mu samar musu da shi in sha Allah,” in ji Huriyya.
Haka kazali, kwamishiniyar harkokin mata da kananan yara da ci gaban jama’a ta jihar, Dakta Nafisa Muhammad Maradun ta ba da tabbacin gwamnatin jihar a shirye ta ke ta gudanar da bikin aure ga marayu ‘yan mata a Gusau.
Don haka Hajiya Huriyya ta yi kira ga al’ummar jihar da su kara yin addu’o’in zaman lafiya a jihar tare da samun nasarar ayyukan gwamnatin ta sa a gaba.