Nan da kasa da mako daya, gwamnoni 20 za su gudanar da bikin cika shekara daya a karagar mulki. Wasu daga cikinsu sun samu nasarar zama gwamnoni ne bisa goyon bayan ubanen gidansu wadanda suka share musu hanya.
A Nijeriya, babewa tsakanin ubangidan siyasa da yaronsa ba sabon abu ba ne.
Wasu daga cikin wadanda suka babe a siyasa sun hada da Rabiu Kwankwaso da Umar Ganduje, Peter Obi da Willie Obiano, Udom Emmanuel da Godswill Akpabio, Adams Oshiomhole da Godwin Obaseki, Rauf Aregbesola da Gboyega Oyetola, da dai sauransu.
A daya bangaren kuma, kila za a iya cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu shi ne ubangidan siyasa da ya fi samun nasara a wannan komawa mulkin dimokuradiyya. Tsakanin 2007 har zuwa yau, ya kafa gwamnoni har guda uku a Jihar Legas, amma har zuwa yanzu shi ke rike da tsarin siyasar jihar.
A ‘yan kwanakin nan, rikici ya kara kamari tsakanin Gwamnan Jihar Ribas, Similayi Fubara da maigidansa da ya gada, Nyeson Wike.
Haka ma lamarin yake a Jihar Kaduna, inda a yanzu haka akwai alaman rikici tsakanin tsohon gwamna, Nasiru el-Rufai da Gwamna Uba Sani. A Jihar Benuwai ma lamarin ba ta sauya zani ba, inda Gwamna Alia da tsohon gwamna, George Akume suke kai rikici kan wanda zai zama jagoran jam’iyya.
Haka zalika, akwai jihohin wasu jihohi da har yau ba a samu sabani tsakanin gwamna mai ci da kuma wanda ya gada. Ko da yake za a iya samun rikicin, amma bai kai ga har a buga a jaridu ba.
Kebbi
Tsohon gwamna, Atiku Bagudu ya goyi bayan Nasir Idris lokacin zaben fitar da gwani, wanda ya doke tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Yahaya Abdullahi.
Kusan shekara daya da kafuwar wannan gwamnati, Bagudu yana daga cikin manyan ministocin gwamnatin Tinubu, wanda har yanzu ba a samu hayaniya ba tsakaninsa da magajinsa kan shugabancin jihar.
Kano
Bayan da ya tsallake rijiya da baya na tsawon shekaru 8 a siyasar magajinsa, tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya zama ubangidan siyasa.
A 2019, Kwankwaso ya yi kokarin dora sirikinsa, Abba Yusuf kan mulkin Jihar Kano, amma bai yi nasara ba. Sai dai a 2023, Kwankwaso ya samu nasarar dora sirikinsa kan karagar mulkin Kano, wanda har yau ba a ji sun samu wani rashin fahimta ba.
Jigawa
Har zuwa yau ba a samu rikici ba tsakanin ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Abubakar Badaru da magajinsa, Umar Namadi ba.
Kamar dai sauran gwamnoni, Badaru shi ya zabi mataimakinsa a matsayin wanda zai gaje shi.
Idan za a iya tunawa, Namadi bai fara gwamnati da Badaru a 20015, ya shiga gwamnati ne lokacin da aka yada Ibrahim Hadeja a 2019.
Sakkwato
Aliyu Wamakko ya kasance cikin shugabancin Jihar Sakkwato tun daga 1999, lokacin da ya zama mataimakin tsohon gwamnan jihar, Attahiru Baffarawa.
Ya goyi bayan Aminu Tambuwal a 2015, amma sun samu rashin jituwan siyasa na wani dan lokaci, inda a bara ya sake goyon bayan Gwamna Ahmad Aliyu.
Har dai zuwa yanzu ba a ji rashin jituwar siyasar a tsakaninsu ba.
Akwa Ibom
Har zuwa yau ba a samu rikicin siyasa tsakanin tsohon gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel da Gwamna mai ci, Umo Eno ba.
Ebonyi
Tsohon gwamnan Jihar Ebonyi kuma ministan ayyuka, Dabe Umahi bai samu rikicin siyasa da shi da maganjinsa, Francis Nwifuru. A daidai lokacin da Umahi ke gudanar da ayyukan da suka shafi tarayya, shi kuwa gwamnan yana tafiyar da ayyukansa na jiha.
Kuros Ribas
Gwamna Bassey Out da ubangidansa, Ben Ayade suna da kyakkyawan danganta wajen gudanar da ayyuka tun bayan kammala zaben bara.
Inugu
Tsohon gwamnan Jihar Inugu, Ifeanyi Ugwuanyi ya goyi bayan, Peter Mbah gabanin zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP a 2022, duk da matsinlambar jam’iyyar LP, har zuwa yanzu dai PDP ke mulki a jihar.
Ugwuanyi ya kasa samun damar shiga majalisar dattawa, sakamakon turjiya daga dan takarar jam’iyyar LP, Okechukwu Ezea.
Sai dai har zuwa yanzu akwai kyakkyawan fahimta tsakanin tsohon gwamnan da kuma wanda ya gaje shi.
Delta
A 2023, a karon farko, dan takarar da James Ibori ya mara wa baya a zaben gwamnan Jihar Delta bai samu nasara ba.
Tsohon gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa ya mara wa, Sheriff Oborebwori baya, wanda ya samu nasarar kayar da dan takarar Ibori, Dabid Edebbie.
Har dai zuwa yanzu ba a samu rikici tsakanin tsohon gwamnan da magajinsa ba.