Gwamnonin jihohi a ranar Laraba sun nuna cikakken goyon bayansu ga matakin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na Cire Tallafin mai.
Gwamnonin wadanda suka yi maganar a lokacin da shugaban kasan ya amshi bakwancin kungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) a karkashin jagorancin shugaban kungiyar, AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara a fadar shugaban kasa, sun yaba wa matakin Tinubun tare da shugabancin da ke janyo Kowa a jika.
A cewar sanarwar manema labarai daga fadar shugaban kasa, Gwamnonin sun kuma taya shugaban kasa Tinubu murna bisa nasarar dakile barnata dukiya da sunan tallafin Mai, sun Yi alkawarin mara baya domin a samu fitar da tsare-tsaren da za su rage wahalar da jama’a ke fuskanta sakamakon cire tallafin.
Tun da farko, shugaba Tinubu ya yi kira ga Gwamnonin da su hada kai da Gwamnatin tarayya wajen shawo kan fatara da talauci da ake fama da shi a kasar nan.
Shugaban ya nemi ‘yan siyasa da su jingine banbance-banbancensu domin hada karfe wajen magance damuwowin da suke addabar al’ummar kasa.
Shugaban kungiyar Gwamnonin Nijeriya kuma gwamnan Jihar Kwara, AbdulRasaq, ya gode shugaban bisa gayyatar da ya musu domin tattauna muhimman batutuwan da za su taimaka wajen shawo kan matsalar talauci da fatara, tsaro inda suka yi alkawarin mara baya domin a samu nasarar shawo kan matsalolin.