Majalisar dokokin Nijeriya ta ce, ta amince da sabbin kudirorin gyaran kundin tsarin mulkin kasar guda 35.
A ranar Talata ne majalisar dattijai ta bukaci magatakardar da ya mika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kudirori 35 daga cikin kudurorin gyaran kundin tsarin mulki guda 44 da aka kawo mata.
Daga cikin sabbin kudirorin da basu sami karbuwa ba, ciki har da kudirin doka na neman ‘yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi a bangaren kudi.