Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP kuma gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana cewa ba su da wani shiri na yin mubayi’a ga gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnonin PDP sun bayyana hakan ne sakamakon yadda shugaban kasa ya sulhunta rikicin siyasar Jihar Riba, a yayin da ‘yan majalisar dokokin jjihar 24 masu biyayya ga ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike suke yi yunkurin tsige gwamna Siminalayi Fubara.
- Kotu Ta Hana NLC Da TUC Shiga Yajin Aiki
- Kasar Sin Na Adawa Da Duk Wani Abu Da Zai Yi Illa Ga Fararen Hula Da Keta Dokokin Kasa Da Kasa
Lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce wanda ta kai har sai da gwamnoni PDP suka ya ba wa shugaban kasa bisa wannan sasanci, inda wasu suke ganin cewa gwamnonin PDP sun mika wuya ga gwamnatin Tinubu.
Gwamnonin sun bayyana hakan ne bayan kammala wani taro da suka gudanar a Abuja.
Sakamakon sulhunta Wike da Fubara wanda dukkansu ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne ya janyo takaddama wanda ya sa har gwamnonin suka mayar da wannan martani.
Jiga-jigan jam’iyyar PDP, musamman magoya bayan dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, kamar irin su mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Daniel Bwala, sun caccaki gwamnonin PDP bisa ziyartar Wike da kuma yaba wa Tinubu.
A cikin sanarwar da kungiyar gwamnonin PDP suka fitar da ke dauke da sa hannun darakta janar na kungiyar, Cyril Maduabum, ta bayyana cewa shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya kuma gwamnan Jihar Kwara, Abdul Rahman Abdul-Razak sun yaba wa Tinubu bisa sulhunta rikicin siyasar Jihar Ribas.
Maduabum ya bayyana cewa daukacin gwamnonin Nijeriya na jihohi 36 sun goyi bayana wannan sulhu, inda wasu suka siffanta lamarin da rashin hankali bisa yaba wa shugaban kasan na shiga tsakani.