• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

by Leadership Hausa
14 hours ago

Saboda kasancewarsa mai sasanta mutane da hada kansu duk da bambance- bambancensu; ga kuma samar da abubuwan more rayuwa a kauyuka, farfado da lamarin kula da lafiyar al’umma, taimaka wa manoma da matasa yadda za su tsaya da kafafunsu; tafiyar da gwamnati ta tausaya wa al’umma, yin biyayya da dokoki, da tunanin yadda gaba za ta yi kyau; shi ya sa aka zabi Sanata Uba Sani a matsayin Gwarzon Gwamnan shekarar 2025.

Ya gaji matsaloli masu yawa amma ya yi ƙoƙari maida su fitila mai kore duhu ta kawo haske.

Gwamnan kowa Yanzu a Jihar Kaduna lamarin ci gaba shi ne gaba, hanyoyi ne zuwa ƙauykan da aka manta, gina asibitoci da sabbin kayan aiki, mutanen kuma da suke ganin da an maida su Saniyar ware yanzu da sune ake damawa a gidan gwamnati.

A duk tsakiyar wannan lamarin ci gaban Sanata Uba Sani ne — ɗan gwagwarmaya, ɗan kasuwa, ɗan majalisa, kuma mai haɗa kan al’umma — wanda kasancewarsa a lamarin sasantawa tsakanin al’umma irin hakan ne yasa ,utane suka dawo hayyacinsu  har ma suka amince gwamnati tana da rawar da zata taka wajen tafiyar da su.

  • Shettima Ya Yaba Wa Uba Sani Kan Kafa Majalisar Ƙwarewa Ta Jihar Kaduna
  • Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 

“Zaman lafiya ba domin babu wata matsala bane kamar yadda ya kan furta,”, “amma kuma adalci ne kan samar da hakan.”

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri

A shekara biyu kaɗai,ya yi ƙoƙarin maida Jihar Kaduna da aka sani da rarrabuwar kai, yanzu ta koma tsintsiya ɗaya sanadiyar hakan.

Yin gyara ta hanyar ci gaba

Gwamna Sani ya hau kan karagar mulki ne a shekarar 2023 ba a matsayin wanda ya iya lamarin siyasa sosai ba, sai dai mai son kawo agyara. Aikinsa na farko ba siyasar bace —mutane ne yafi maida hankali kansu.

Ya fara ƙaddamar da lamarin gaggarumin ci gaban ƙauyuka ta yadda abin ya zama a kowace ƙaramar hukumar akwai aikin da ake yi.Gina hanyoyi, asibitoci,  makarantu, kasuwanni an fara gigginasu a ƙananan hukumomi  23 .

Cikin ci gaban daya samu sun haɗa da:

Haɓaka ƙananan asibitoci 225 inda aka mayar da su matsayi na 2, inda tuni aka kammala 174.

An gyara 13 daga cikin manyan asibitoci 33 da kuma sa masu dukkan kayan da suka kamata.

Gadaje 300- na asibitin ƙwararu, da aka yi watsi da shi tun shekarar 2009, an kammala su, Shugaban ƙasa Bola Tinubu — ya ƙaddamar dasu inda aka kawo ƙarshen shekara 16- da aka yi ana jira.

Manyan motoci 400 da suke ɗauke da Takin zamanin da aka rabawa ƙananan manoma 100,000 kyauta, domin samun ingantaccen abinci maikyau da kuma isasshe.

Kowane aikin da aka yi akwai labarain da yake badawa na dalilin da yasa aka yi shi — na gwamnan da shi manufarsa ita ce kowanne al’umma a Jihar Kaduna.,ko  a Birni suke ko kuma ƙauye, su san da cewa ba mantawa aka yi dasu ba.

Abubuwan more rayuwa ta hanyar sasantawa

Babban burin shi mai sauƙi ne babu wata wahala: ci gaba shi ne babban lamarin tafiya da haɗin kai domin sasantawa.

Yadda aka yi ayyukan a dukkan faɗin Jihar ba tare da la’akari da Kabila ba ko kuma addini, ballantana ma har ace daga wace shiyya mutum yake, ya koyar da amincewa da yarda a cikin Jihar duk kuwa yadda take da al’umma daban- daban.

A ƙoƙarinsa na haɓaka hanyoyi, kilomitoci na manyan hanyoyi yanzu an haɗa su, waɗanda a shekarun baya an raba mutane da zuwa kasuwannin ƙauyuka. Gadoji waɗanda suka haɗa  garuruwa— yanzu sun koma wata dabarar sake haɗa al’ummar da a da basu ga maciji koi zaman manja da doya tsakaninsu, domin da a rabe suke sanadiyar rashin jituwa.

Kaduna a halin da ake ciki yanzu babu wata maganar rarrabuwar kai sai dai ƙarin danƙon- zumunci.

Mai son bunƙasar Mata da Matasa

Gwamna Sani bai tsaya anan ba domin kuwa suma Mata da matasa abin ci gaban ya same su domin kuwa ba mantawa ya yi dasu ba.

A hanyar gidauniyar Uba Sani, an horar da dubban matasa wajen koyon sana’oi, koyon yadda za’a tafiyar da na’urar sadarwa ta zamani, da kuma dabarun sana’oi daban- daban. An kuma raba masu tallafin yadda za su fara sana’oi da wasu kayayyaki waɗanda zasu ɗaukaka mata daga dogaro da wasu, su zama masu nema ba dai a nemo a basu ba.

Hakanan ma ya buɗe hanya inda har ila yau ya taimakawa mata da matasa waɗanda aka sa su wasu wurare masu amfani, inda yake nuna cewa yadda Jihar zata kasance, a gaba abin ya dogara ne kan dukkan al’ummarta gaba ɗaya.

Ya san yadda zai yi mu’amala da mutane

Kafin ya shiga gidan gwamna, Uba Sani ya fara rayuwar zuwa gidan gwamnati ne da zama da zama ɗan gwagwarmaya, ɗan kasuwa, da kuma ma’aikaci —lamarin da kowa yake haɗa hakan ba, shi yasa kuma yadda yake tafiyar da gwamnatinsa abu ne mai sauƙi gare shi.

Ƙuniya mai zaman kanta : A matsayin mataimakin  shugaban na ( Arewa) fafutukar kamfen na damukuraɗiyya, daga baya kuma mataimakin Shugaba  (Arewa)  na JACON ada ke ƙarƙashin Chief Gani Fawehinmi, a  Arewacin Nijeriya zamanin mulkin soja.

Kasuwanci: Ɗan kasuwa ne wanda ya samu nasara a harkar  sadarwa  da kuma gidaje da filaye, daga can ne ya koyi haƙuri idan ya samu riba ko kuma faɗuwa.

Gwamnati: Matsayin Sanata (2019-2023) , yayi shugbancin kwamitin Banki, Inshora da sauran hukumomi masu harkar kuɗaɗe ya bada gudunmawa wajen gyaran da aka yi wanda shi ne ya ƙara haɓaka lamarin kuɗaɗe.

Irin halayya ta gwagwarmaya, kasuwanci, da kum atsarin manufofi hakan ya samar da Shugaba kuma jagora, wanda idan aka aikata rashin adalci zai nuna rashin adalci, akwai ranar da zai nemi ayi zaman sulhu.

Mai ra’ayin ilimi, yin abu yadda ya dace ayi shi, da kuma mutuntawa

An haife shi ranar 31 ga Disamba 1970, a Zariya, Sani yana digiri na biyu a harkokin da suka shafi kuɗi daga Jami’ar Kalaba, sai Difiloma kan harkokin mulki daga Jami’ar Abuja , da kuma Babbar Difiloma ta ƙasa kan  Makanikal Injiniya daga makarantar  fasaha ta Kaduna.

Hakanan ma shi shi tsohon ɗalibi ne na  wani karatun da yayi kan Shugabanci  a Amerika. (IƁLP) “yin abu ba tare da amsar ko kwabo ba, sai yadda za ‘a tafiyar da ƙungiyoyi masu zaman kansu.”

Karatuntukan makarantun da yayi ko shakka babu sun kasance fitila gun shin a yadda zai tafiyar da harkokin gwamnati da dai sauran al’amura.

Daga majalisa zuwa gidan gwamnati

A matsayin san a Sanata, Uba Sani ya bar wani abinda ya zama tarihi. Uku daga cikin ƙudurorinsa sun samu amincear Shugaban ƙasa — lamarin da ba kowa bane zai samu irin wannan sa’ar — hakan ne ma yasa ake girmama shi a matsayin ɗan majalisa da yafi amfani a majalisar ƙasa ta 9.

Sa’oin daya samu sun nuna cewar horon ya yi matuƙar taimaka ma shi wajen yadda yake tafiyar da mulkin Jihar Kaduna.

Yanzu shi ne, mataimakin ƙungiyar gwamnonin APC shi ne kuma gwamna da zai sa ido kan lamauran sashen Arew a maso yamma, da kuma daidaituwar manufofin gwamnatin tarayya da Jihohi.

Shugaba mai sauraren jama’arsa

A Jihar Kaduna, koda waɗanda basu yin shi sun amince da gwamna Uba Sani ya na tafiyar da mulkinsa kamar yadda ya dace.

Yana ganawa da al’umma kafin motar da zata yi gyara ta kama aikinta, zai saurare su kafin ya ɗauki mataki, a wurin shi kuma dole ne tilastawa ta biyo bayan tausayawa.Yadda yake sauraren al’umma yasa suna amincewa da duk waɗansu abubuwan daya kawo gabansu tsakanin Sarakunan gargajiya, Shugabannin addini, da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Ba wani abin mamaki bane tunda yanzu tarurrukan zaman lafiya yanzu sun fi zanga- zanga, ga kuma uwa- uba yadda ake haɗa kai tsakanin al’ummomi shi ne ya maye gurbin yadda ake zama a shekarun baya.

Ayyukan da ya yi sun sa amincewa da yadda yake

Gwamnan Kaduna Uba Sani ba wai ya fi kowa iya mulki bane, amma akwai ci gaba a Jihar saboda da akwai yarda juna, wanda ta hakan ma ana samun ci gaba.

Mulkinsa ya maida hankali ne kan abubuwan more rayuwa, kula da lafiyar al’umma, aikin moma, da kuma masana’antu, irin hakan ne ya jawo hankalin al’umma a iyakokin Nijeriya.

Shi ya sa mutane ke son tun daga zucci, ɗan gwagwarmayar da ya taɓa yi zanga- zanga domin a wanzar da mulkin farar hula —yanzu shi ne mai gina damukuraɗiyya da hanyoyi, makarantu, da kuma asibitoci.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar
Manyan Labarai

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

October 24, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu
Manyan Labarai

Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Irin Ministocin Da ‘Yan Nijeriya Ke Tsammani Daga Gwamnatin Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

October 24, 2025
Next Post
Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025

Gwamnatin Katsina Ta Ƙara Samar Da Dakarun Tsaro 200 Domin Maganace Ta’addanci

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

October 24, 2025
An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

October 24, 2025
Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 

Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 

October 24, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.