• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwmana Lawal Ya Bayyana Wa UNICEF Shirin Jihar Zamfara Na Ƙaddamar Da Dokar Kare Al’umma 

by Sulaiman
10 months ago
UNICEF

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana aniyar gwamnatinsa na ƙaddamar da shiri, tare da Dokar Kare Al’umma, musamman ƙananan yara da raunana a duk faɗin jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnan ya karbi baƙuncin wakilin Asusun Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, a Nijeriya da sauran masu hannu da shuni a gidan gwamnati da ke Gusau.

  • Kwanaki Bayan Kashe Masunta 20, Boko Haram Ta Kashe Sojoji 20 A Borno
  • Me Ya Sa A Ko Da Yaushe Mutane Suke Karkata Hankalinsu Ga Kasar Sin A Davos?

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa Cristian Munduate, wakilin UNICEF a Nijeriya, ya bayyana jin daɗinsa dangane da ci gaban da ake samu a fannin kiwon lafiya a Zamfara.

Sanarwar ta ƙara da cewa, UNICEF, GAVI, WHO, da wakilan Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya sun halarci taron yaɗa dokoki da manufofin zamantakewa na jihar Zamfara.

A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya jadadda cewa, tsarin Daidaiton Jinsi na jihar Zamfara wani muhimmin mataki ne na wargaza wariya tare da samar da yanayi mai kyau ga kowane jinsi wajen samun ci gaban rayuwa.

LABARAI MASU NASABA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

“Baya ga tsarin Daidaiton Jinsi, muna kuma ƙaddamar da Dokar Kare Al’umma a jihar Zamfara. Waɗannan matakai suna da muhimmanci don tabbatar da cewa tsarin zamantakewarmu yana da ƙarfi kuma ya dace da buƙatun mutanenmu, musamman ma masu rauni.

“Dokar kare haƙƙin yara da dabarun aiwatar da ita sun ƙarfafa ƙudurinmu na kare haƙƙin yara da walwalarsu. A matsayinsu na ginshiƙin makomarmu, dole ne mu tabbatar da cewa yara suna cikin aminci da kulawa don cimma burinsu.

“Dokar nakasassu ta jihar Zamfara ta nuna ƙudurinmu na kare haƙƙin nakasassu. Wannan na neman kawar da wariya da haɓaka damar shigarsu cikin al’umma. Mun haɗa da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da nakasassu, don tabbatar da jin muryoyinsu.

“Saboda haka, za a sake duba dokar don ƙara haɗa kai, kuma za a kafa kwamitin da zai magance takamaiman buƙatun nakasassu.”

Gwamna Lawal ya ƙara jaddada cewa gwamnatinsa ta tsinci fannin kiwon lafiya a cikin wani mawuyancin hali a jihar.

“Don cimma burinmu na samar ingantacciyar kiwon lafiya kuma mai araha daidai da tsarin duniya, mun ayyana dokar ta-baci a bangaren kiwon lafiya.

“Misali, ta hanyar Hukumar Raya Al’umma da Ci Gaban Jama’a (CSDA), gwamnatin jihar ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya 61, ciki har da manyan asibitoci 10, sannan ta shiga tsakani a wasu cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 51.

“Tare da tallafin gwamnatin jiha kai tsaye, mun gyara tare da inganta asibitin ƙwararru na Yariman Bakura da manyan asibitocin Talata Mafara da Shinkafi, inda muka mayar da su Manyan Asibitocin Ƙwararru na yankin.

“Mun kuma fara gina cibiyar VVF don kula da matsalolin mata masu juna biyu tare da amincewa da gina cibiyar gwaje-gwaje a matsayin wani bangare na ƙudurinmu na samar da ingantaccen kiwon lafiya.

“Ƙoƙarin da muke yi, tare da goyon bayan dukkan abokan hulɗarmu, ya riga ya fara samar da sakamako mai kyau a dukkan tubalan gina tsarin kiwon lafiya.

“Mun yi nasarar dakatar da yaɗuwar cutar shan inna a jihar Zamfara, kuma mun samu raguwar bullar cututtukan da za a iya magance su ta hanyar rigakafi, kamar su kyanda, sankarau, da zazzabin rawaya. A shekarar 2024, jiharmu ta samu bullar cutar Diphtheria guda biyu kacal duk da barkewar annobar a jihohin makwabta.

“Mun kuma ba da gudunmawa sosai wajen gyara Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Ungozoma da ke Gusau da kuma gyara Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Lafiya da ke Tsafe.

Gwamnan ya yaba da haɗin gwiwar UNICEF da jihar, kuma ayyukan sun yi matuƙar tasiri.

“A kan tasirin da GAVI ya yi a jiharmu, muna godiya musamman da yadda ku ka haɗa cibiyoyin kiwon lafiya 50 na mu da na’urorin wutar lantarki masu amfani da hasken rana, wanda ke ba su damar samar da ayyuka na sa’o’i 24 cikin inganci.”

“Wannan aikin yana haɓaka ƙarfinmu don adanawa da rarraba alluran rigakafin zuwa wurare daban-daban. Zuba jarin ku a rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da ban-ɗakuna a cibiyoyin kiwon lafiya 29 yana inganta jin daɗin ma’aikata da marasa lafiya, yana kuma ƙarfafa alaƙar al’umma ga wuraren kiwon lafiya.

“Muna godiya da goyon bayanku na shigar da mata da yara marasa galihu 33,000 cikin tsarin inshorar lafiya na jihar. Wannan aikin yana ɗaya daga cikin ayyuka mafi tasiri da aka taba yi, kuma mun sadaukar da kai don ci gaba da samun nasarori.”

A farko, Cristian Munduate, wakilin UNICEF a Nijeriya, ya ce wannan ne karo na farko a duniya da GAVI ta yanke shawarar tallafa wa tsarin kiwon lafiya na ƙasa da ƙasa. “Mun yi farin ciki saboda an ga sakamako mai kyau a Zamfara, kuma wannan zai sa GAVI ta ci gaba da tallafa wa ayyukan kiwon lafiya a irin wannan matakin ba kawai a cikin ayyukan ƙasa ba.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna
Labarai

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga
Labarai

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra
Labarai

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Next Post
Bikin Bazara Na Kasar Sin Na Samun Karbuwa Daga Masu Yawon Shakatawa Na Duniya

Bikin Bazara Na Kasar Sin Na Samun Karbuwa Daga Masu Yawon Shakatawa Na Duniya

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.