Hukumar gudanarwa ta babban birnin tarayya (FCTA) tana shirin kashe naira biliyan daya wajen gyaran babban masallaci da cocin da ke garin Abuja.
Ministan Abuja, Muhammed Bello shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya ci gaba da bayyana cewa a halin yanzu dai kudaden shiga na Abuja yana karu zuwa biliyan 200 a duk shekara.
Ministan ya kara da cewa za a kashe naira biliyan 500 a kan kowanni wurin ibada na addinan biyu ne domin tsare wuraren Ibadan daga farmakin ‘yan ta’adda.
Ya ce garin Abuja yana kara bunkasa a halin yanzu, wanda ake ta samun karuwar kudaden shiga na haraji.
Ya ce, “Za mu yi amfani da abubuwan da muke da su a hannu wajen tsare babban birnin tarayya, domin akwai wuraren da suke bukatan samun kariya.
“Muna matukar kokari wajen tara kudaden shiga domin mu kawata birnin Abuja da ababen more rayuwa wajen kara habaka garin.”
Bello ya yaba wa jami’an tsaro wajen gudanar da kyakkyawan aiki na kula da garin Abuja.
“Jami’an tsaro suna matukar kokarin a Abuja. Duk abubuwan da suke faruwa da a Abuja wadanda muke ji a kafafen yada labarai, kosan kashi 10 zuwa 15 sun zama tarihi.”
Sai dai ya bayyana cewa za a ci gaba da gudanar da rusau a cikin Abuja domin sake dawowa da cikakken tsarin birnin.
“A yau mun rushe wasu yankuna a garin Abuja, kuma za mu ci gaba da yin hakan saboda duk yadda muka yi kokarin tabbatar da doka da oda, sai mun samu mutane masu kunnen kashe da za su karya doka,” in ji Bello.