Za ki tafasa alimun, bayan kin wanke duk wani jini dake dankarewa mace na haihuwa, to kuma sai ki wanke jikinki da ruwan alimun ki kuma shiga ciki ki zauna tsawon minti goma sannan ki fito, a nan a gefe ki samu naman da kika dan dafa ki cinye da dumi sai ki dora da kununÂ
Kunun aya, Kunun kanwarki, Kunun gyada
- Ma’aikatar Cinikayya Ta Sin Ta Yi Karin Haske Game Da Soke Takunkumin Da Amurka Ta Kakabawa Sin
- Sin: Tsawaitar Rikicin Ukraine Ba Zai Amfani Kowa Ba
Gyaran gaba a lokacin al’ada:
lokacin al’ada lokacin ne da mace za ta tsaya ta kula ta ga cewa ba ta sakin jikinta kamar lokuta da ba ta al’ada ba, musamman ma budurwa wacce ba ta taba aure ba, har ita ma matar auren wacce ta san ciwon kanta, kuma ba ta son ta ga miji ya yi watsi da ita da wuri ko yana tunanin karin aure da wurin, to sai ki tsaya ki maida hankali wajen kulawa da jikinki a lokacin al’ada da kuma haihuwa, saboda ita ce mace a duk lokacin da take cikin al’ada to a wannan lokacin jikinta budewa yake yi, shi ya sa idan mace na cikin al’ada idan akwai manya a kusa, sai su rika hana ta daukan abu mai nauyi
Bokiti da kuma tsalle-tsalle ko kazar-kazar saboda wannan lokacin jikinta a bude yake.
Idan ko tana wannan kazar-kazar din to dukkanin jikinta budewa yake yi.
Don haka idan budurwa ta yi aure kuma ta kasance mai irin wannan dabi’a shi ne sai ki ga an sami matsala da miji yana zarginta da ko tana yawon banza tun da bai same ta a matsayin wacce ba ta taba aure ba.
Nan kuwa ba haka bane, yawan tsalle-tsalle ne ya jawo a yayin al’ada.
Idan kuma matar aure ce to sai ka ga jikinta ya sake budewa, idan ta gama al’ada ta koma turaka sai ki samu maigida bai damu da ya rika waiwayarta ba saboda a madadin jikinta ya matse a a sai ma ya kara budewa da yayi.
Don haka idan har kina cikin al’ada ya kamata ki kula da irin zaman da zaki yi da tafiya ki kuma kiyaye da daukar abu mai nauyi.
Yadda za ki gyara:
Ya zama dole ki kula da wanke mafi karanci a rana sau biyu wato safe da yamma.
Sannan wanka da sabulun mai kamshi da kuma ruwan dumi, sai kuma ki shafa mai mai kamshi ki saka turare mai kamshi, sannan a koda yaushe ki rika yawan canja din da ke jikinki saboda shi jini ya danganta, wani yana karni wani babu wani ma wari yake.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp