Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.
A yau shafin na mu zai kawo muku yadda za ku magamce kaushin kafa, duba da yanayi ya sauya mun shigo yanayi na san yi, Allah ya fitar da mu lafiya. ‘yar uwa kada ki kuskura ki bar kafarki da kaushi ko faso, zanin gadonki ya zama kamar kafarki, wasu za su ce akwai faso na ciwo wasu kuma su ce fatarsu ce mai gautsi, to, ai ana neman maganin kaushi da fatso.
- Sin Ta Yi Maraba Da Amincewar Da UNGA Ya Yi Da Kudurin Wanzar Da Zaman Lafiya Da Kasar Ta Gabatar
- Kalubalen Rashin Tsaftar Muhalli A Nijeriya
Akwai na Hausa, akwai na asibiti, sai ki zabi wanda za ki yi amfani da shi.don illar kaushi da faso ba ta tsaya a nan kadai ba, don yana ragewa mace ni’ima sosai, to ko don wannan a nemi magani ki kula da abubuwan da za su kara miki ni’ima da nishadi.
Abubuwan da za ki tanada don gyaran kafa, kafa tayi laushi, tayi kyau sosai. Wasu matan rashin tsabta ce, yayinda wasu matan hallitace, haka koma dai menene ga mafita.
Ku samu kofi daya na ruwan Khal a hada da lemon tsami, sai a shafe kafar kullum sau biyu a rana bayan an wanke kafar da minti sha biyar sai a shafe ta da Zaitun za’a ga abin mamaki.
Ruwa san yi da gishiri a tsoma kafar a ciki zuwa minti sha biyar sai a wanke a shafa Zaitun, amma sai kafafun sun bushe.
Wasu hanyoyin gyaran faso da kaushin kafa
Fason kafa ya kan zamewa mutane karfen kafa musamman ma a lokacin san yi, ko a yankunan da suka fi bushewa fiye da wasu. Wannan yana faruwa ne saboda fatar kafa ta fi ta sauran sassan jiki bushewa kuma tana bukatar kulawa ta musamman wanda yawancin lokuta ba ta samu.
Rashin kula da faso ka iya ta’azzara shi ta yadda zai iya fara jini, ko ciwo ko kuma kwayoyin cuta su shiga ciki.
Ga wasu hanyoyi biyu masu sauki da za’a iya magance wannan matsala
Hanya ta farko: Amfani da Ruwan Kal (Farin Binegar ko Apple Cider Binger) Za a zuba ruwa a cikin babbar roba, sannan a zuba ruwan Kal kamar 1/4 na kofi daya. Sai a jika kafar a ciki na tsahon minti 10 zuwa 15. A yi amfani da dutsen kaushi wajen gurje fatar da ta jiku, sai a yi amfani da farin ruwa wajen dauraye kafar.
Bayan an goge ta da tawul mai tsafta, sai a shafa man kwakwa, ko Zaitun ko kuma man Kadanya, za a maimata sau uku a sati.
Hanya ta biyu: Amfani da baikin soda za a zuba ruwa a roba mai fadi sannan a zuba coKali uku na baikin soda a ciki a saka kafar a ciki na tsahon minti 15 sannan a yi amfani da dutsen kaushi wajen gurje ta. A dauraye da farin ruwa a goge ta da Tawul mai tsafta.
A shafa mai shima ana maimatawa kamar sau uku a sati. Za a iya samun baikin soda a wuraren da ake sayar da kayan hada kek wata cake ko kuma manyan shaguna ko manyan kantina, Shi kuma ruwan Kal an fi samun shi a manyan kantina ko kuma shagon magani na musulinci.