Gidauniyar ‘TY Buratai Literary Initiative (TYBLI)’ ta kaddamar da shirye-shiryen tallafinta na 2025 wanda ta kudiri aniyar bunkasa ilimi da tsarin koyo a tsakanin daliban Nijeriya.
Shirin wanda gidauniyar Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) ta kirkiro kuma ta dauki nauyin wannan shiri na da nufin kwadaitar da koyon Adabin rubutu da kuma bai wa daliban da suka fi hazaka tukuici a fadin kasar nan.
- Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kashe Naira Tiriliyan 4.2 Don Aikin Manyan Hanyoyi
- Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kashe Naira Tiriliyan 4.2 Don Aikin Manyan Hanyoyi
Da take jawabi a wani taron manema labarai, Dokta Lizi Ben-Theanacho, shugabar Gidauniyar ta TYBLI, ta jaddada kudirin Gidauniyar na bunkasa adabin rubutu ta hanyar samar da littattafai da kyaututtuka ga dalibai masu hazaka.
“Abu na farko da muke fatan aiwatarwa shi ne, mu ba da gudummawa don samar da ilimi mai zurfi a Nijeriya ta hanyar samar da littattafai, tabbatar da ingancin kayan karatun da suka dace. Daga nan, sai mu zakulo dalibai masu hazaka, mu gwangwaje su da kyaututtuka na ban mamaki.
“TYBLI Gidauniya ce ta wayar da kan jama’a da bayar da tallafi ga al’umma wacce Laftanar Janar TY Buratai (mai ritaya) ya kirkiro kuma ya dauki nauyin aiwatarwa.” in ji ta.