Farfesu wani abu ne mai kwantar da hankali da kuma dawo dadandano na baki. Wannan Farfesun na ji dadin sa ni da iyali na har ma sun bukaci in sake musu saboda ya ba da dandano mai dadi ga kuma ya yi kyau a ido ga mai ci zai ji dadin cin sa. Yar uwa ki gwada za ki gode min.
Abin da uwargida za ta tanada domin hada wannan farfesu
Karfashen kifi manya guda, Albasa babba sai a gurza ta, Kren Tattasai guda biyu, Jan Tattasai guda biyu, Karen Taruhu uku, Tumatir daya, Tafarnuwa manya uku, Citta danya kadan, Dandano daidai bukata, Gishiri, kayan kamshi, Na’a na’a kadan, Albasa mai lawashi, Korinyanda kadan, Black Pepe.
Idan uwargida ta tanadi wadannan abubuwan za ta hada su gaba daya a tukunya sai ta yi musu dahuwar farfesu yadda ake yi, amma dai wannan ya banbanta da sauran.
Da fatan uwargida ta fahimta a ci dadi lafiya.