Kwanakin baya, Sanata Ahmad Bola Tinubu, ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban tarayyar Najeriya. A lokacin da na fara aiki a birnin Lagos dake kudancin Najeriya a shekarar 2006, Bola Tinubu ya riga ya kwashe shekaru 7 yana aiki a matsayin gwamnan jihar Lagos.
A karkashin jagorancinsa, an gina dimbin hanyoyin mota masu inganci a jihar, wadanda suka burge wani abokina da ya zo ziyara jihar ta Lagos daga yankin gabashin Afirka a lokacin. Yanzu haka bisa matsayinsa na shugaban kasa, mista Tinubu ya sanya burika na samar da karin guraben aikin yi, da rage talauci, da ci gaba da gina kayayyakin more rayuwa, da dai sauransu.
Za mu gane ma idanunmu yadda sabuwar gwamnatin kasar Najeriya za ta yi kokarin cimma burikan da ta sanya gaba cikin shekaru masu zuwa. A sa’i daya kuma, na san kasar Sin za ta iya taka rawa a cikin wannan kokarin da ake yi.
A kwanan baya, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Peng Qinghua, ya gana da shugaba Tinubu, inda ya ambaci burin Sin na hada manyan tsare-tsaren raya kasa tare da kasar Najeriya. Wannan na nufin, za a ci gaba da kokarin inganta huldar hadin kai ta amfanar juna tsakanin Sin da Najeriya, wanda kuma zai taimakawa sabuwar gwamnatin Najeriya wajen cimma burinta na raya kasa.
Me ya sa na fadi haka?
Dalili shi ne, da farko, cinikin da ake yi tsakanin Najeriya da Sin na ta karuwa a wadannan shekaru, wanda ya zama wani tushe ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya. Yanzu haka, Najeriya ita ce abokiyar ciniki ta kasar Sin mafi girma ta 3 a nahiyar Afirka, yayin da Sin ita ce kasar da Najeriya ta fi shigar da kayayyaki.
Daga shekarar 2016 zuwa ta 2021, yawan cinikin da ake yi tsakanin Najeriya da Sin ya karu da kimanin kaso 142%. Kana a shekarar 2021, darajar kayayyakin da aka fitar da su daga Najeriya zuwa kasar Sin ta kai dalar Amurka biliyan 3.04, adadin da ya karu da kashi 22.4% bisa na shekarar 2020.
Na biyu shi ne, kasar Sin tana kokarin zuba jari a Najeriya, da mika mata fasahohi, lamarin da ke samar da gudunmowa ga kokarin gwamnatin Najeriya na raya masana’antu da samar da guraben aikin yi. Najeriya tana cikin kasashen Afirka da suka fi janyo jari daga kasar ta Sin. Kuma ya zuwa shekarar 2021, yawan jarin da kasar Sin ta zuba ma Najeriya ya riga ya zarce dalar Amurka biliyan 20, wanda ya shafi ayyukan da suka hada da gina yankunan ciniki masu ‘yanci, da na sarrafa kayayyakin da ake fitar da su zuwa ketare, da hako danyen mai, da samar da kayayyakin latironi da motoci, da aikin gona, da dai sauransu. Cikinsu, yankunan ciniki masu ‘yanci na Lekki, da na Ogun-Guangdong, da kamfanonin kasar Sin suka gina, sun riga sun janyo jarin da ya zarce dalar Amurka biliyan 1.51, tare da samar da guraben aikin yi fiye da 7000.
Na uku shi ne, kasar Sin na taka muhimmiyar rawa bisa kokarin Najeriya na gina kayayyakin more rayuwa. Wasu kamfanonin kasar Sin fiye da 20 sun dauki nauyin gina wasu manyan kayayyaki masu muhimmanci a fannonin raya tattalin arzikin Najeriya, da inganta zaman rayuwar jama’ar kasar, wadanda suka shafi layin dogo, da hanyoyin mota, da aikin samar da wutar lantarki, da sadarwa, da tace danyen mai, da dai makamantansu. Zuwa yanzu, wasu manyan kayayyakin da kamfanonin kasar Sin suka gina, irinsu layin dogon da ya hada Abuja da Kaduna, da wanda ya hada Lagos da Ibadan, da sabbin gine-ginen filayen saukar jiragen sama na wasu manyan biranen kasar, da tashar jiragen ruwa ta Lekki, da tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa dake Zungeru, dukkansu na taimakawa Najeriya samu ci gaba a fannonin tattalin arziki da zaman al’umma.
Na hudu shi ne, ta hanyar hadin gwiwa da kasar Sin, Najeriya za ta iya samun karin damammakin raya tattalin arziki, bisa amfani da yarjejeniyar da ta kulla tare da sauran kasashen dake nahiyar Afirka, ta gina wani babban yankin ciniki mai ‘yanci a nahiyar, wato AfCFTA. Da ma bisa la’akari da yanayin da kasar Najeriya ke ciki na rashin karfin masana’antu, inda ake sa ran ganin kasar za ta halarci tsarin AfCFTA a matsayin wadda ke shigar da kayayyaki daga sauran kasashen dake nahiyar Afirka. Lamarin da zai takaita ribar da kasar ka iya samu ta AfCFTA.
Har ma wani binciken da aka yi ya nuna cewa, ribar da Najeriya za ta iya samu duk shekara daga AfCFTA, za ta kai dala miliyan 146, yayin da kudin da Afirka ta Kudu za ta samu zai kai dala biliyan 1.46. Dalilin da ya sa haka, shi ne domin kasar Afirka ta Kudu wata babbar kasa ce a fannin samar da kayayyaki. Saboda haka, idan Najeriya na son samun karfin takara a kasuwar bai daya ta Afirka, da sanya tattalin arzikinta samun damar karuwa cikin dorewa, to, dole ne a yi iyakacin kokarin raya masana’antu. Sai dai kasar Sin a nata bangare tana kokari zuba jari ga kasuwannin Najeriya don raya masana’antu a can, wanda hakan muhimmin bangare ne ga yunkurin kasashen Najeriya da Sin na hada tsare-tasaren su na raya kasa.
Ba shakka, hadin gwiwar da ake yi tsakanin Najeriya da Sin shi ma zai amfani kasar Sin. Kuma yanayin wannan hulda ta amfanar kowa ya sa ta iya dorewa. Kaza lika kasancewar kasashen suna hadin kai da juna ne bisa wani yanayi na daidai wa daida, shi ya sa “ Tattaunawa tare, da gina harkoki tare, gami da cin moriya tare” suka zama wata babbar manufa ta hadin gwiwar da ake yi.
A kokarin raya tattalin arziki da al’umma, kasashen Najeriya da Sin suna hada hannu, suna neman ci gaba kafada da kafada, ba tare da wata kasala ba. (Bello Wang)