Nahiyar Asiya da Afirka muhimmin mafari ne na wayewar kan bil Adam, inda yawan mutane da suke da su ya kai kashi 70% na dukkanin al’ummun fadin duniya. Yau shekaru 70 da suka gabata, taron Bandung mai taken “Dunkulewa da zumunci da hadin gwiwa”, ya ingiza niyyar kasashen wadannan shiyyoyi na dogaro da kansu da hadin gwiwa, matakin da ya aza tubalin neman adalci, da daidaito, da hadin gwiwa a huldar kasa da kasa.
Kazalika, yau shekaru 10 da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana ra’ayinsa a taron kolin kasashen Asiya da Afirka, wato burin farfado da raya wannan sassa, ta yadda za a kafa sabuwar huldar kasa da kasa bisa tushen hadin gwiwa da cin moriya tare, an kuma kai ga wannan ra’ayi a matsayin matakin dake gada ruhin Bandung.
- An Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Masu Jan Hankalin Xi Jinping” A Kasar Malaysia
- Yaukaka Zumunci Da Makwabta A Aikace Tsakanin Sin Da Malaysiya
Sin ba ma kawai mai gabatar da wannan ra’ayi ba ce kadai, a daya fannin ta taka rawar gani wajen ba da jagorancin aiwatar da shi. Sin da abokanta na wadannan sassa sun kyautata yanayin huldar duniya, sun yi amfani da tsarin hadin gwiwar mabambantan bangarori, da kuma ingiza daidaita harkokin duniya tsakanin bangarori daban-daban a maimakon tsarin da aka bi a baya wato na kasashen yamma su yi jagoranci, har sun ba da misali irin na Asiya da Afirka na sauya salon bunkasar duniya daga “tunani na wani bangare daya dake samun riba, ta yadda wani bangare na daban tilas ya yi hasara”, zuwa “tunanin hadin gwiwa da cin moriya tare”.
Wato na farko, dogaro da kai a bangare makamashi, shawarar “ziri daya da hanya daya” ta kafa wani tsarin tattalin arziki dake amfanar da dukkan kasashen Asiya da Afirka, sun kuma kara karfin kafa tsare-tsaren samar da kayayyaki na mabambantan bangarori a shiyyar ta hanyar kara tuntuba, da dunkulewar manyan ababen more rayuwa, da yin musayar fasahohi, wanda hakan ya sa kasashen ba sa dogaro da sana’ar fitar da makamashi kawai, matakin da ya kara musu kwarin gwiwar samun bunkasuwa da kansu.
Na biyu, samun jari da kansu. Sabon bankin raya mambobin BRICS, da bankin zuba jari na Asiya da dai sauran hukumomi, sun baiwa kasashe masu tasowa wata hanyar samun jari na daban ban da kasashen yamma. Ya zuwa shekarar 2025, bankin zuba jari na Asiya ya amince da ba da rancen kudi da yawansu ya kai dalar biliyan 44.7, an zuba kashi 58% daga cikinsu a kasashe ko yankuna marasa ci gaba a bangaren kafa manyan ababen more rayuwa, ta yadda ba sai sun dogara da IMF da sauran hukumomi irinsa su kadai ba.
Na uku, daidaita manufofin cinikin duniya. Hadin gwiwar ciniki cikin ’yanci na Afirka da RCEP, ya rarraba aikin samar da kayayyaki ga bangarori daban-daban, kuma hakan ya gaggauta raguwar harajin kwastam tsakanin kasashe da batun ya shafa da kashi 37%. Kazalika, ya kawar da matsin lamba, da barazana da kasashe wasu wadata ke haifarwa kasashe masu tasowa ta amfani da shingayen ciniki. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp