Babban mai bincike a fannin huldar kasa da kasa da harkokin diflomasiyya, karkashin cibiyar nazarin harkokin waje ta kasar Habasha Melaku Mulualem, ya ce hadin gwiwa tare da kasar Sin, karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya” ko BRI, ya taimaka matuka wajen inganta rayuwar al’ummun kasar Habasa.
Mulualem ya ce, a matsayinta na daya daga jerin kasashen dake hadin gwiwa da kasar Sin karkashin shawarar BRI, Habasha ta cimma gajiya daga ribar shawarar a fannin kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar miliyoyin ’yan kasar.
Masanin ya kara da cewa, “Shawarar BRI ta inganta rayuwar da dama daga jama’ar Habasha. ’Yan kasar da yawa sun samu guraben ayyukan yi karkashin manyan ayyukan da ake aiwatarwa karkashin shawarar, ciki har da sashen raya masana’antu na kasar, da tashoshin jiragen kasa, da manyan hanyoyin mota, da ayyukan sadarwa na dijital da dai sauransu. Wadannan ayyuka sun yi matukar bunkasa tattalin arzikin kasarmu.” (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp