Bisa kididdgar da aka bayar, yawan nakiyoyin da aka binne a karkashin kasa da suka rage a wurare daban-daban a duniya bayan yake-yake ya kai miliyan 110, lamarin dake zama kalubale ga tsaron duniya. Nahiyar Afirka ma, wuri ne mafi fama da wannan mummunar matsala. An ce, yawan nakiyoyin da aka binne a karkashin kasa da suka rage a kasashen Afirka 19 ya kai kimanin miliyan 37. A kasar Mozambique, rabin nakasassu sun gamu da wannan matsala ne saboda fashewar nakiyoyin. A Angola kuma, ko wani mutum daya cikin mutane 236, ya rasa hannu ko kafa sanadin fashewar nakiyoyin.
Ana daukar tsaro da muhimmanci saboda shi ne kashin bayan samun bunkasuwa. Sin ta dade tana dukufa kan taimakawa al’ummar Afirka wajen kawar da nakiyoyin da aka binne a karkashin kasa don tabbatar da jin kai, inda ta dauki matakai na tallafa wa Habasha da Angola da Eritrea da kuma Chadi da sauransu, wajen inganta kwarewarsu ta kawar da nakiyoyin, don kare tsaron jama’ar kasashen da ciyar da bunkasuwar tattalin arziki da zaman al’umma gaba. Sai kuma a gun taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da ba a dade da rufewa ba a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da aiwatar da aikin taimakawa nahiyar Afirka kawar da nakiyoyin da aka binne a karkashin kasa, don share wannan kablule daga nahiyar.
Hadin gwiwa a bangaren tsaro wani muhimmin sashe ne na tabbatar da kyakkyawar makomar Sin da Afirka ta bai daya a ko da yaushe. Sin za ta dukufa kan aiwatar da ayyuka a wannan fanni karkashin tsarin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka, ta yadda za a daga karfin kasashen Afirka na kare zaman lafiya da kwanciyar hankali, da ma shimfida wani yanayi mai kyau ga kasashen wajen tabbatar da tsaro da karko da kuma ci gaba mai dorewa. (Mai zane da rubutu: MINA)