Ministan kudi na kasar Ghana Kenneth Ofori-Atta, ya ce hadin gwiwar Sin da kasarsa, ya kasance mai matukar muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin kasar ta yammacin Afrika.
Cikin jawabin da ya gabatar da yammacin ranar Talata a wani biki da aka yi albarkacin cika shekaru 74 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, Ofori-Atta ya yabawa kasar Sin bisa dimbin goyon bayanta ga kasar Ghana a dukkan fannonin tattalin arziki, ciki har da taimakawa kasar samun rancen dala biliyan 3 daga asusun bada lamuni na duniya.
Haka kuma, ministan ya ce Ghana ta ci gajiyar hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin ababen more rayuwa da ilimi da tsaro da aikin gona da sadarwa da kiwon kifi. (Fa’iza Mustapha)