Yayin da kasashen Afirka ke kara mayar da hankali ga kyautata dangantakarsu da kasar Sin, da ma yadda sassan biyu ke kokarin cika alkawuran da suka yiwa juna, na bunkasa cudanya, da cimma moriya tare, karkashin muhimman shirye-shirye da suka amincewa, muna iya cewa kwalliya tana kara biyan kudin sabulu yadda ya kamata.
Ko da a ranar Alhamis ta makon jiya, mahukuntan kasar Zimbabwe sun kaddamar da aikin fadada tashar lantarki ta Hwange, wadda ke amfani da tururi wajen samar da makamashin lantarki, a yankin Hwange mai nisan kilomita 780 daga birnin Harare, fadar mulkin kasar.
Kamfanin Sinohydro na kasar Sin ne ya dauki nauyin gudanar da aikin da tallafin gwamnatin kasar Sin, wanda bayan kammala karin manyan injunan sarrafa lantarki 2 a tashar, yanzu haka injunan da tashar ke aiki da su sun kai guda 8, matakin da zai bunkasa yawan lantarkin da kasar za ta rika samu daga wannan tasha, matakin da zai yi tasiri ga raya masana’antun kasar, da fadada guraben ayyukan yi.
Ko shakka babu, kammala wannan muhimmin aiki sakamako ne na hadin gwiwa mai ma’ana tsakanin Sin da Zimbabwe, kamar dai yadda sauran kasashen Afirka ma suke cin gajiya daga makamantan wadannan ayyuka na raya kasa, da more rayuwar al’ummun kasashen.
Masharhanta da dama na jinjinawa kwazon gwamnatin kasar Sin, da sahihiyar aniyar kasar ta tallafawa ayyukan more rayuwa da dama, da take daukar nauyin gudanarwa a Afirka, da ma sauran kasashe masu tasowa a sassan duniya daban daban.
Irin wadannan ayyuka, na shaida kyakkyawan zumunci, da kaunar juna dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, yayin da dukkanin sassan biyu ke kara amincewar juna ta fuskar cinikayya, da musayar ilimi da al’adu, da sauran manyan fannonin kyautata rayuwar bil adama, daidai da burin da Sin ta jima tana yayatawa, na tabbatar da gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga daukacin bil adama. (Saminu Hassan)