Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce hadin gwiwar da Sin ke yi da kasar Rasha, ba ta da nasaba da kaiwa wata kasa ta daban hari, ko tsoma baki cikin harkokin wata kasa, ko muzgunawa wata kasa ta daban. Mao Ning ta bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa na yau Talata.
A yau Talatar ne, yayin taron dandalin kasuwanci na Sin da Rasha, wanda ya gudana a birnin Shanghai, firaministan Rasha Mikhail Mishustin ya bayyana cewa, duk da kasancewar hadin gwiwar Sin da Rasha zai haifar da moriyar tattalin arziki ga kasashen 2, a hannu guda mai yiwuwa wasu kasashen yammacin duniya su nuna damuwa, ko rashin amincewa da wannan kyakkyawan hadin gwiwa, ko ma su fara tunanin kakaba takunkumi, bisa lura da batutuwan da suka shafi kasar Rasha.
Game da hakan, Mao Ning ta ce har kullum kasar Sin na gudanar da harkokin ta na raya tattalin arziki da hadin gwiwar cinikayya da Rasha, da ma sauran kasashen duniya yadda ya kamata, karkashin jigon daidaito, da cimma moriyar juna, kuma a ko da yaushe kasar Sin na adawa da kakaba takunkumi na kashin kai, da yankewa kasashen ketare hukunci, irin wanda ba shi da hurumi a karkashin dokokin cudanyar kasa da kasa, kuma bai samu amincewa daga kwamitin tsaron MDD ba.(Saminu Alhassan)