• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Kara Wa Mace Ni’ima Da Sha’awa Da Karin Dandano

by Bilkisu Tijjani
12 months ago
Mace

Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.

A yau shafin na mu zai kawo muku yadda za ku kara wa kanku ni’ima da dandano.

  • Kakakin Ma’aikatar Tsaron Sin Ya Yi Tir Da Sayar Da Makamai Da Amurka Ke Yi Wa Taiwan
  • CMG Ta Gabatar Da Shirye-Shiryen Talabijin A Peru

Macen da ke so ta rikita mai gida to ga hanya mai sauki, ke ko mota kike so in dai ki ka yi wannan hadi to fa kin samu, amma fa idan an samu mota kar a manta da ni.

Hanyar kuwa itace:

Kayan hadi:

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

Hadin Tsumin Baure

Dabino, kwakwa (coconut), Nonon Rakumi, Zuma

Yadda za ku hada:

Da farko za ki cire kwallon dake cikin dabino, sai ki kawo kwakwarki bayan kin bare bayanta ki samu ruwa kadan ki zuba a kai ki nika su.

Bayan kin gama sai ki kawo zuma kamar rabin kofi, nonon Rakumi kamar kofi daya ki hada da kwakwar nan da kika hada da dabino ki hade da zuma da nonon Rakumin waje daya.

Ki rika sha kadan-kadan kamar tsawon kwana 7 za ki ba da labari.

Hadin zuma:

Abubuwan da ake bukata:

Zuma, Garin Habbatussauda, Man Zaitun

Yadda zaki hada

Karin ni’ima da motso sha’awa za ki sami Zuma mai kyau ki zuba garin Habbatus-sauda da man Zaitun ki juye su guri guda sai ki dinga sha babban cokali biyu da safe da kuma yamma.

Hadin dayan kwai:

Yana karawa mace kuzari ba tare da ta gaji ba wajen jima’i kuma yana kara wa mace ni’ima da sha’awa.

Abubuwan bukata:

Lifton, danyen kwai, zuma, a jika Lifton da ruwa kadan har sai ya yi baki, sai ki fasa kwai ki hada shi, ki zuba cikin ruwan Lifton kina iya zuba madara Peak sai ki zuba zuma ki dinga sha.

Karin ni’ima.

Za ki iya yin shayin kara karfin sha’awa da ni’ima yadda za ki yi shi ne, ki samu sassaken baure ki daka shi sai ki daka kanunfari ki hada da Lefton kina sha za ki yi mamaki.

Gyara kanki da kanki:

Maganin sanyin mara da rashin ni’ima;

Macen da take fama da sanyin mara ko daukewar sha’awa ko rashin ni’ima ga abin da za ta hada in sha Allah za ta samu waraka.

Garin Girfa (Cinnamon), garin kanunfari (clobe)

Za a samu garin girfa kamar cokali 5 garin kanunfari cokali 7 za ki hade waje daya, sai ki rika diban rabin karamin cokali kina zubawa a ruwan shayi kina sha sau 2 a rana har na tsawon sati daya. Za a samu waraka da yardar Allah.

Domin karin ni’ima:

Kamar yanda mata ke ajiye zuma a gida haka yanzu mata ba sa rabuwa da kanumfari domin duk wani hadin daka na musamman ko hadin ruwan jaraba ko wani tsumi idan kuka bincika, za ku ga akwai sa hannun kanumfari don haka kema ki ajiye shi don burge maigida duk lokacin da za ki dafa shayi kada ki manta da shi domin idan ya hadu da lifton yana aiki ajikin mace wajen karin ni’ima kuma yana da kyau a jinki ya zama akwai kanumfari a ciki.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Hadin Tsumin Baure
Ado Da Kwalliya

Hadin Tsumin Baure

September 27, 2025
Gyaran fuska
Ado Da Kwalliya

Gyaran Fuska Da Laushin Fata

August 30, 2025
Next Post
Yadda Ake Kosan Filantan

Yadda Ake Kosan Filantan

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

Matashi Ya Kashe Ɗan Acaɓa Don Neman Kuɗin Auren Mace Ta Uku A Bauchi

October 17, 2025
katsina

Tawagar Bankin Duniya Ta Gana Da Gwamnan Katsina Kan Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira Muhallinsu

October 17, 2025
Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

October 17, 2025
Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari

Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari

October 17, 2025
Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

October 17, 2025
Abduljabbar

Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja

October 17, 2025
An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

October 17, 2025
Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

October 17, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn

October 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.