Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta tura wata kakkarfar tawaga kasar Saudi Arabiya don nema wa Nijeriya karin kujeru a aikin hajin bana.
Tuni Kwamishina aikin hajji mai kula ayyuka, Abdullahi Hardawa, ya gana da mataimakin Minista mai kula da aikin Hajji da Umara a kan lamarin ranar Lahadi.
A tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, , Hardawa ya ce, an mika wa hukumar kasar Saudiyan bukatar kujera 5,000, saboda karin al’umma su samu sauke farali a bana.
“Ina Saudiya a halin yanzu ne don neman karin kujeru wanda muka tura bukatar haka tun kafin a fara harkokin aikin hajjin bana.
“Daga sauka na Riyadh na wuce don ganawa da Ambasadan mu wanda ya bayyana mani irin kokarin da yake yi a kan lamarin.
“Sun tabbatar mani da cewa, za su amince da bukatarmu tunda mun riga mun rubuta musu, sun yi alkawarin cika biya mana bukatar mu.
“Muna bukatar wadannan kujerun ne domin kamfanonin masu jigilar alhazai da kuma maniyyata a jihohi da kuma gwamnatin tarayya.
“Bamu taba tunanin za a nemi karin kujerun hajji ba saboda yadda aka kara kudin zuwa hajjin a bana,” in ji shi.
Ya kuma kara da cewa, ziyararsa zuwa kasa mai tsarki ya yi ne don a kara karfafa bukatar samun kujerun aikin hajjin don al’umma da dama su samu zuwa sauke faralin.