Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, ta ce maniyyata 156 ba za su samu tafiya aikin hajjin bana ba sakamakon yawan kujerun aikin hajji da jami’an hukumar da aka kora suka sayar.
Hukumar Alhazai ta kasa ta ware wa Jihar Kano kujeru 6,144 amma hukumar ta sayar da karin kujeru 156.
- Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri Da Sanusi A Fadar Shugaban Kasa
- Tinubu Ya Nada Ribadu Da Wasu A Matsayin Masu Ba Shi Shawara
Babban daraktan hukumar, Alhaji Laminu Rabiu ne ya bayyana hakan a yayin zanta wa da manema labarai a Kano.
Ya ce, za a binciki jami’an da ke da suka gabata tare da gurfanar da su gaban kuliya da zarar an kammala aikin hajjin bana.
Rabi’u, ya yi kira ga maniyyatan da abin ya shafa da su yi hakuri, ya kuma yi musu alkawarin cewa za a ba su kulawa a aikin hajji mai zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp