Wani kamfani dan kasar Saudiyya mai suna Mashariq Al Dhabia, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar aiki aka yi wa kwaskwarima da hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) domin hidima ga Alhazan Nijeriya a lokacin aikin Hajjin 2025.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, kamfanin a baya ya yi barazanar maka NAHCON a kotu bisa zargin karya sharudan kwangilar da hukumar ta rattaba wa hannu kan hidima ga Alhazan Nijeriya a Masha’ir a lokacin aikin Hajjin 2025.
- Al’ummar Katsina Sun Koka Da Taɓarɓarewar Hanya Da Ƙarancin Ruwan Sha
- Al’ummar Katsina Sun Koka Da Taɓarɓarewar Hanya Da Ƙarancin Ruwan Sha
Amma a wani al’amari mai ban mamaki, sai aka hangi wata tawaga daga kamfanin na Saudiyya a karkashin jagorancin shugaban kamfanin, Muhammad Hassan, ta ziyarci babban ofishin hukumar ta NAHCON da ke ‘Hajji House’ a Abuja ranar ranar Asabar, 22 ga watan Yuli, domin rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangilar da aka sabunta.
Da yake jawabi bayan rattaba hannun, shugaban hukumar ta NAHCON, Farfesa Abdullahi Seleh Usman, ya bayyana cewa, sabunta yarjejeniyar ya zama dole domin gyara wuraren da aka samu kuskuren fahimta da kuma tabbatar da gudanar da ayyukan hajji cikin sauki da samun nasara.
Ya kuma tabbatar wa da dukkan maniyyatan Nijeriya cewa, NAHCON ta kammala shirye-shiryenta, tare da yin watsi da duk wata muguwar magana kan zargin soke kwangilar aikin.
Muhammad Hassan, shugaban Mashariq Al Dhabia, ya bayyana godiyarsa ga NAHCON tare da bayar da tabbacin yin hidima ƙayatacciya ga Alhazan Nijeriya.