Biyo bayan daukan mataki da hukumar kula da alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta yi na kara naira miliyan 1.9 kan kudin aikin hajji na 2024, maniyyata da dama sun nuna matukar damuwarsu tare da neman a dawo musu da kudinsu da suka biya na mallakar kujeru tun da farko.
Hakan na zuwa ne yayin da fitattun kungiyoyin fararen hula da masu ruwa da tsaki suka yi kira ga Shugaban kasa Bola Tinubu da ya ceto aikin hajjin bana daga rashin samun mahalarta.
- Ya Kamata Gwamnati Ta Haramta Wa Mata Baza Jarirai A Titinan Kano – Sarkin Dillalan Kano
- Kisan Okuama: Baƙin Cikin Da Ke Tattare Da Labarin
A ranar Lahadi ne, hukumar NAHCON ta kara naira 1, 918,032.91 na kudin zuwa aikin hajji a kasa mai tsarki kuma wa’adin rufe wannan karin zuwa ranar 28 ga Maris na 2024 ne.
Maniyyatan za su kara kudi ne kan naira miliyan 4.9 da suka biya tun da farko a matsayin kudin kujerar aikin hajji. Inda a cewar hukumar alhazai kowanni maniyyaci zai biya naira miliyan 6.8 domin samu kujerar zuwa hajji.
A wata sanarwa da kakakin hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce karin ya zama dole ne bisa tashin dala da sauran dalilai.
Sai dai maniyyata da daman gaske sun nuna kaduwa da jin sanarwar karin kudin tare da neman a dawo musu da miliyan 4.9 da suka biya tun da farko da cewarsu sun hakura da tafiya aikin hajjin.
Binciken da aka yi a ofisoshin hukumomin jin dadin alhazai a jihohin arewa da na kudanci ya nuna cewa maniyyata kalilan ne zuwa yanzu suka nuna cewa za su iya cire kudin da aka umarta da su biya, yayin da wasu da dama kuma suka ce sai dai a dawo musu da kudin da suka biya sun hakura domin ba za su iya kara biyan wani miliyan 1.9 ba.
Wani maniyyaci daga Jihar Kano, Mustapha Ahmad, ya ce, ya yi fatan cewa koda sau daya ne zai je ya sauke farali a kasa mai tsarki, amma duk da son da yake yi na hakan burinsa ba zai iya cika ba da wannan labarin karin kudin kujera da ya samu.
Haka zancen yake ga ita ma Hafsat Yusuf inda ta ce karin kudin ka iya hanata zu-wa aikin hajji, “Na kadu sosai, muna jiran hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta sanar da nata karin, amma ban san ya za a iya mu iya zuwa da wannan karin ba.”
Haka zalika, Hajiya Rakiya Abubakar daga Jihar Kano ta ce ko barci ba ta iya yi ba lokacin da ta samu labarin karin kudin aikin hajji domin ta gama sanyawa a ranta cewa za ta je aikin hajji ba.
A Jihar Kwara, majiyoyi daga hukumar jin dadin alhazai ta jihar ta nuna cewa maniyyata da dama suna fatan a dawo musu da kudinsu domin ba za su iya biyan wani karin kudi ba. Haka zancen ma yake a jihar Legas domin maniyyata da dama sun nemi a dawo musu da kudinsu muddin sai sun yi kari.
Matukar in ba wai gwamnatin tarayya ta dauki matakin gaggawa ba, sama da maniyyata ‘yan Nijeriya da ke da burin sauke farali a shekarar 2024 za su iya rasa damarsu na halartar aikin hajji a kasa mai tsarki.
Wata kungiyar ‘yan jarida Musulmai a Nijeriya (MMWG) ita ce ta yi wannan anka-rarwar biyo bayan karin kudin aikin hajji na naira miliyan 1.9 da hukumar kula da alhazai ta Nijeriya ta yi ga masu niyyar aikin hajji kan kudin da suka biya a baya.
Ko’odinetan kungiyar na kasa, Alhaji Ibrahim Abdullahi shi ne ya shaida hakan, tare da cewa, za a samu mafita kan wannan matsalar ne kawai idan gwamnati ta dauki matakin rangwamen farashin dala zuwa naira kan aikin hajjin bana ta yadda kudin da maniyyatan suka biya da fari zai kai matakin da za su je Makkah domin sauke farali.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa a ranar Lahadin da ta gabata ne hukumar NAHCON ta sanar da cewa, kowani maniyyacin da ya biya kudin ajiya na naira miliyan 4.9 domin tafiya aikin hajji, yanzu zai sake kara naira miliyan 1.9 biyo bayan tashin gwauron zabin farashin dala.
Sai dai ko’odinetan MMWG wanda ya zanta da jaridar LEADERSHIP dangane da sakamakon bayan taron ganawa na gaggawa da kungiyar ta yi a Abuja, ya ce, “Muddin in ba rangwamen farashin dala zuwa naira aka yi ba, zai yi matukar wahala ga sama da maniyyata ‘yan Nijeriya 50,000, wadanda suka biya kudinsu ajiyarsu tun watannin ba, su samu damar halartar aikin hajji na ba.”
A cewarsa, gwamnati ta zauna ta rangwanta kan musayar canjin kudi a kan aikin hajji kowace shekara ba wannan ne farau ba, inda ya ce, gwamnatocin baya a Ni-jeriya sun sha yin hakan.
Abdullahi, daga bisani, ya yi kira da babban murya ga shugaban kasa Bola Tinubu da a cikin gaggawa ya shigo cikin batun domin kawo mafita, wanda a cewarsa la-marin na neman addabar masu ruwa da tsaki a harkar hidimar hajji.
Ya tunatar da gwamnatin tarayya da cewa ta fa gane cewa aikin hajji ibada ne da ya zama wajaba a kan masu hali, don haka akwai bukatar gwamnatin ta kyautata rayuwar al’umman da take mulka da saukaka musu lamura, ya kara da cewa, akwai kuma bukatar gwamnati ta tashi tsaye wajen kawo karshen matsalolin kuncin rayuwa da matsin tattalin arziki hadi da matsalar tsaro da ke addabar kasar nan a halin yanzu.
Ya ci gaba da cewa, “Rangwamen farashin zai taimaka sosai wa nasarar shi kansa Tinubu ta yadda maniyyatan da za su samu zuwa aikin hajjin za su yi wa shugaban kasa da gwamnatinsa addu’ar shawo kan matsalolin da suke addabar Nijeriya idan sun je kasa mai tsarki na Makkah da Madinah.”
Daga karshe ya jinjina wa hukumar NAHCON bisa kokarinta na ganin an samu sauki cikin lamarin, ya roki masu niyyar sauke farali da su yi hakuri har zuwa loka-cin da za a samu shawo kan lamarin.