Wani abin da ke ci gaba da dauke hankalin mabiya kwallon kafa a gasar cin kofin duniyar da ke gudana a Katar shi ne, yadda dan wasan Morocco, Achraf Hakimi ke rugawa wajen mahaifiyarsa yana sumbatar ta da zaran sun kammala wasa.
Dan wasan kungiyar PSG da ke kasar Faransa na daya daga cikin zaratan ‘yan wasan Morocco da ke ci gaba da samun nasara a wasannin na Katar, ganin yadda suka kawar da manyan kasashe irinsu Spain da Portugal.
Hakimi na daga cikin wadanda suka taka gagarumar rawa wajen kai Morocco zuwa matakin wasan kusa da na karshe da suka fafata a ranar Laraba da tawagar Faransa mai rike da kambun gasar.
Sai dai bayan zama daya daga cikin tauraron ‘yan wasan Morocco, Hakimi na dauke hankalin ‘yan kallo da kuma masu bibiyar kasarsa a gasar ta yadda da zarar an kammala wasa ya kan ruga wurin mahaifiyarsa domin sumbatarta a cikin ‘yan kallo.
Yayin da yake tsokaci a kan wannan mataki da yake dauka, Hakimi ya ce iyayensa sun sadaukar da rayukansu wajen taimaka masa zuwa kai wa matakin da yake yanzu, saboda haka ba zai yi watsi da su ba, abin da ya sa yake alfahari da su ko da yaushe.
Dan wasan ya ce mahaifiyarsa ta yi aikatau a gidajen jama’a domin biya masa bukatu, yayin da mahaifinsa kuma yake sayar da kaya ne a titi domin samar musu abin da za su ci.
Hakimi ya ce wannan sadaukarwar da suka masa wajen aiki tukuru har ya kai shi matakin da yake yanzu ba zai ba shi damar juya musu baya ba, saboda haka yake alfahari da su ko da yaushe.
Ya zuwa wannan lokaci, Hakimi mai shekaru 24 ya yi nasarar buga wasu daga cikin manyan kungiyoyin kasashen Turai irin su PSG da Inter Milan da Borussia da Dortmund, inda ake bayyana shi a matsayin daya daga cikin fitattun ‘yan wasan baya na duniya.