• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hakkin Makwabtaka Muhimmin Abu Ne Da Ya Kamata Japan Ta Yi La’akari Da Shi

by CMG Hausa
2 years ago
Japan

Yayin taron hukumar kare hakkin bil adama ta MDD karo 53 dake wakana, kasar Sin ta sake kira ga Japan da ta dakatar da shirinta na zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku. Ko a makon da ya gabata, kasar Sin ta yi irin wannan kira, tana cewa bai kamata Japan ta dauki rahoton IAEA a matsayin izini aiwatar da nufin nata ba. 

Ba yanzu kasar Sin da sauran kasashe makwabta suka fara bayyana damuwa dangane da wannan batu ba, lallai ya zama wajibi Japan ta sake nazari game da kudurin nata don ganin ba ta sa son rai a ciki ba. Hakkin makwabtaka babban abu ne, domin a ko da yaushe, makwabta ne ke iya kai dauki na farko-farko idan bukatar hakan ta taso, haka kuma babu wanda zai iya tserewa duk wata annoba da za ta shafi makwabcinsa. Kamata ya yi Japan ta yi nazari, ta kuma duba korafin makwabtanta domin suna da hakki a kanta, kana ta yi la’akari da wasu al’ummominta da su ma suke adawa da matakin nata.

  • Sin Ta Bukaci Japan Da Kada Ta Yi Yunkurin Amfani Da Rahoton IAEA A Matsayin Izinin Zubar Da Dagwalon Ruwan Nukiliya A Cikin Teku

Idan Japan ta yi gaban kanta tare da biyewa kasashe masu hure mata kunne, lallai mummunan tasirin abun da za ta aiwatar ba zai tsaya kan makwabtanta ba, ita kanta za ta dandana kudarta, don haka, gudun kar a yi, to kar ma a fara.

Kamar yadda kasar Sin ta bayyana, bai kamata Japan ta dauki rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) ta fitar a matsayin izinin zubar da dagwalon nukiliya cikin tekun ba, domin alamomi sun nuna cewa, an yi gaggawar fitar da rahoton, kana ba a sanar da dukkanin masanan da suka yi nazarin sakamakon ba. Ko kadan gaggauta fitar da rahoto game da muhimmin batu irin wannan bai dace ba, kuma ba zai haifar da da mai ido ba, domin akwai abubuwa da dama da ya kamata a yi la’akari da su duba da cewa, ya shafi al’ummomi da dama.

Abu mafi dacewa shi ne, Japan ta dakatar da shirin, ta hada kai tare da tuntubar masana daga kasashen makwabtanta da ma hukumar IAEA, domin sake gudanar da nazari wanda zai kasance bisa gaskiya da adalci da ilimi, su daddale, su lalubo mafita mafi dacewa da za ta karbu ga dukkan bangarori, ba tare da cutar da wani ba, haka kuma wadda za ta dore. Kana, Japan ta daina sauraron zugar kasashen yamma wadanda kansu kadai suka sani, kana ba su da masaniya ko ma ba su damu da yanayin da shirin zai iya jefa al’ummar yankin ba. (Fa’iza Mustapha)

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne
Daga Birnin Sin

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Next Post
An Yi Wa Mataimakin Shugaban Nijeriya Osinbajo Tiyata A Kafarsa

Bayan Sati 6 Da Barin Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Osinbajo Ya Samu Sabon Mukami

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

November 8, 2025
Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.