• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hako Man Fetur: Jihar Neja Ta Nemi Hadin Gwiwar Kamfanin Dangote

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
5 months ago
Fetur

Tare da kwararru a fannin makamashi, rukunin Dangote na da muhimmiyar rawar da zai taka wajen ba da gudummawa ta fuskar bunkasa wuraren da aka gano mai kwanan nan a yankin Bida na Jihar Neja.

Da yake jawabi ga shugabannin masana’antu a taron bikin baje kolin kasuwancin kasa ta Jihar Neja da aka yi a Minna, Gwamna Bago ya sanya Jihar Neja a matsayin wata cibiya ta kasuwanci” dangane da bunkasar mai na a tafkin ‘Bida Basin’, musamman ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su zuba jari da kwarewa a aikin hako mai da iskar gas a jihar.

  • Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin
  • Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya

Gwamna Umaru Muhammed Bago wanda ya samu wakilcin Hamza Bello Sarki babban sakataren ma’aikatar kasuwanci da masana’antu da saka hannun jari, ya amince da kwazon da kamfanin DDangote ke da shi wajen gudanar da manyan ayyukan masana’antu, inda ya ba da misali da nasarar isar da matatar mai a kasar nan daya tilo da aka yi a Nijeriya a matsayin shaida ta kwarewar fasaha da kuma kyakkyawan aiki.

Rukunin Dangote shi ne kan gaba wajen daukar nauyin bikin baje kolin kasuwanci na Nijar na 2025.

Gwamnan ya bayyana gano mai yankin na Bida Basin a matsayin tikitin Jihar Neja na bunkasar tattalin arziki, da cin nasara ga abokan hulda.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

Wani rahoto na binciken yanayin kasa na shekarar 2023 ya gano bututun mai guda 17 da za aiya cin kasuwa da shi a Jihar Neja, tare da kiyasin da aka yi na zai hako iskar gas har ta tsawon shekara 70.

Basin na Bida, wanda ya ratsa sassan jihohin Neja da Kwara, an gano shi a matsayin yankin da ke kwararo albarkatun mai mai cike da fa’ida.

Wakilin rukunin Dangote, Mista Hashem Ahmed, ya ce kamfanin yana zuba jari sosai a Jihar Neja, ya kara da cewa a shirye yake ya hada gwiwa da jihar domin ba ta damar bunkasa abubuwan da ta ke da su.

“Kamfanin Shinkafa na Dangote da ke Wushishi idan an kammala shi zai inganta noman shinkafar cikin gida da kuma rage asarar da ake samu bayan girbi, muna kuma aiki kafada da kafada da ofishin gwamna kan shirin samar da abinci na Neja, shirin noma da ke taka muhimmiyar rawa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu
Manyan Labarai

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole
Labarai

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU
Labarai

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Next Post
Wang Yi Ya Nanata Matsayin Taiwan Yayin Tattaunawa Da Takwaransa Na Faransa

Wang Yi Ya Nanata Matsayin Taiwan Yayin Tattaunawa Da Takwaransa Na Faransa

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

October 20, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.