Jam’iyyun siyasa 18 ne suka yi rijista da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), a lokacin da aka gudanar da babban zaben shekarar 2023. Koda-yake, guda bakwai ne kadai a cikinsu suka iya samun kujeru daga kan zaben shugaban kasa, gwamnoni, majalisun dokoki na kasa da kuma majalisar jiha. Wadannan jam’iyyu sun hada da APC, PDP, LP, NNPP, SDP, APGA da kuma YPP.
Gasa Da Kece Raini
‘Yan takara 18 ne suka nemi kujerar shugabancin kasa, inda har ila yau kimanin ‘yan takara 1,904 suka fito neman kujerun majalisar dattawa, wadda take da membobi 109. Kazalika, kimanin ‘yan takara 3,244 ne suka nemi kujerun majalisar wakilan kasar nan mai dauke da membobi 435, sannan ‘yan takara 416 ne suka nemi kujerun gwamnoni a jihohi 28 da aka gabatar da wadannan zabubbuka, yayin da kuma ‘yan takara kusan 10,240 suka fito neman kujerun majalisar jihohi 990a fadin jihohin Nijeriya.
Adadin kafatanin kujerun da aka fafata wajen zawarcinsu a zaben 2023, sun kai kimanin 2,533, yayin da kiyasin 16,808 suka fafata domin neman kujeru daban-daban, a wannan takaitaccen bayani, banda batun zaben fitar da gwani na gwamnoni da kuma na majalisun jihohi guda takwas.
Har ila yau, a kujerun shugabannin kananan hukumomi 774, a kowace jam’iyya akwai dan takara guda daya, wanda idan aka lissafa zai bayar da ‘yan takarkaru kimanin13,932, haka nan kididdigar kujeru 14,500 na kansiloli, wanda zai tasamma kimanin ‘yan takara 70,000 na wadannan jam’iyyun siyasa 18 da ake da su a fadin kananan hukumomi 774.
Kazalika, APC da PDP sun samu sama da kashi 90 cikin 100 na kujeru a matakin tarayya da jihohi, yayin da sauran suka samu kashi 10 cikin 100; inda kuma mafi yawansu suka kasa samun wata kujera ko yin wani gagarumin tasiri.
Halin Manyan Dawakai
– Kudade da albarkatu masu yawa: Manyan jam’iyyun, sun samu damar samun makudan kudade daga wurare daban-daban. Sannan, sun kuma samu damar kashe makudan kudaden a wajen yakin neman zabe tare da yin tasiri ga masu kada kuri’a. Abin taikaici a nan shi ne, wasu naira dari kacal suka karba, wasu kuma taliyar indomi domin zaben dan takara.
– Rashin tsari da iya warware rikici. Kamar yadda ta faru, ga wasu babu tsari amma sun samu damar warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu tare da gabatar da dan takara guda daya tilo, ko dai ta tilastawa ko kuma wani nau’i na matsin lamba.
Matsalolin Kananan Dawakai
– Rashin isassun kudade da kayan aiki: Wasu ba su da isassun kayan aiki domin gudanar da yakin neman zabe, haka nan biyan kudaden tallace-tallacen kafafen yada labarai, shirya tarurruka tare da tara magoya bayansu. Har ila yau, ba su da isassun kayan aiki da kayayyakin more rayuwa, don isa ga masu kada kuri’a a fadin kasar baki-daya.
– Karancin goyon bayan jama’a: Kananan jam’iyyun siyasa ba su da isasshen wakilci ko tasiri a cikin kafofin watsa labaru, kungiyoyin jama’a da sauran dandamali wadanda za su iya taimakawa wajen samun nasara a zabe.
– Rikicin cikin gida da rarrabuwar kai: Sau da dama suna fama da rikice-rikicen cikin gida da rarrabuwar kawuna, wanda ya raunana damar samun nasara. Wasu daga cikin jam’iyyun kuma sun fuskanci rikicin shugabanci da sauran makamantansu.
– Rashin adalci a zabuka: Ko shakka babu, kananan jam’iyyu sun fuskanci cikas da kalubale daban-daban a harkar zabe. Wasu daga cikin kalubalen sun hada da tashe-tashen hankula da kuma tsoratarwa, wanda ya hada da magudi, satar kuri’u, sayen kuri’u da kuma rashin ingancin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), da kuma dokar zabe da sauran makamantansu.
Tasiri a nan gaba
- Shin kananan jam’iyyu za su iya yin tasiri a irin wannan yanayi na siyasa da a ciki?
- Shin akwai hikima a fannin tattalin arziki a ci gaba da wannan harkar ko kuwa manyan dawakai ne ke ciyar da kananan dawakai?
- Shin dabi’ a ce mai kyau a cikin dabi’u a koyaushe a ga ‘yan siyasa suna tsalle daga wannan jamÃya zuwa wancan kamar yadda ya ke faruwa a Nijeriya yanzu, sannan ya kamata ‘yan Nijeriya su amince da hakan?
Inna mafita
Shin zai yiwu a kubutar da ’yan Nijeriya yayin da ake ganin kamar sun samu kwanciyar hankali a cikin bautar da suke ciki?
–     Eh, mai yiyuwa ne a fita daga wannan mawuyacin hali da rugujewar akidar siyasa, inda kashi 90 cikin 100 na ‘yan siyasar Nijeriya, ba kasar ce a gabansu ko ‘yan kasar ba, sai san kansu da zalunci.
–     Bugu da kari, ya rage wa sauran kashi 10 cikin 100 na ‘yan siyasa masu hankali da kishin kasa da su canza salon siyasar kasar, domin talaka ya samu ya numfasa.
 Bayanan karshe
Tarihi ya nuna sau da dama an fi samun ‘yan siyasar da ke rike da madafun iko, bayan sun sauka ko kuma damar ta kubuce musu su zama abun tausayi, ko samun kansu cikin wani yanayi na lahaula ko wani abu mai kama da haka.
Kukan kurciya dai hausawa sun ce jawabi ne.
Alhaji Adamu Rabiu, ya rubuto daga Kaduna.