Rahotanni sun ce Hamas ta amince da sharuddan tsagaita bude wuta da Isra’ila, wadda ke kai hare-hare ta kasa da ta sama a Gaza a matsayin ramuwar gayya kan harin ranar 7 ga Oktoba, 2023.
A lokacin farmakin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra’ila, ta yi garkuwa da mutane da dama a Isra’ila inda ta kawo su Gaza, wanda hakan ya haifar da ramuwar gayyar da ta yi sanadin mutuwar Falasdinawa kimanin 46,000.
- Da Ɗumi-ɗumi: Sojoji Sun Haramta Amfani Da Jirage Marasa Matuƙa A Arewa Maso Gabas
- Ayyukan Ba Da Agaji Abin Koyi Daga Kasar Sin A Girgizar Kasa A Jihar Xizang
A ranar Laraba, jami’an Isra’ila da na Falasdinu sun ce Hamas ta amince da yarjejeniyar sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma dakatar da kai hare-hare a Gaza.
Rahotanni daga kafafen yada labarai da dama na cewa, jami’an Isra’ila sun yi nuni da cewa, bangarorin biyu sun cimma matsaya kuma nan ba da dadewa ba za a iya fara aiwatar da yarjejeniyar.
Sun kara da cewa, mai yiyuwa ne a fara aiwatar da yarjejeniyar a ranar Lahadi. Ana sa ran Hamas za ta saki Isra’ilawa 33 da ta yi garkuwa da su a matakin farko na yarjejeniyar yayin da za a sako daruruwan fursunonin Falasdinawa daga gidajen yarin Isra’ila a lokaci guda.