Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta inganta hadin gwiwa a aikace tare da Saliyo a fannoni daban daban, da hada kai wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya.
Han ya bayyana hakan ne a birnin New York na kasar Amurka, a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio a gefen babban taron MDD karo na 78.
Ya bayyana cewa, kasashen Sin da Saliyo ‘yan uwa ne kuma abokai na kwarai, wadanda ke abota na aminci da goyon bayan juna, kuma a ko da yaushe bangarorin biyu suna goyon bayan juna matuka kan batutuwan da suka shafi muhimman moriyarsu da manyan batutuwan da suka shafi juna.
Han ya kara da cewa, kasar Sin tana taya Saliyo murnar zama mambar da ba na din-din-din ba a kwamitin sulhu na MDD daga shekarar 2024 zuwa ta 2025.
A nasa bangare shugaba Maada Bio ya godewa kasar Sin, bisa taimakon da take baiwa kasarsa cikin shekaru da dama, yana mai cewa, kasar Sin aminiyar al’ummar Saliyo ce. Ya ce, Saliyo na martaba ka’idar Sin daya tak a duniya, kuma a shirye take ta inganta hadin gwiwa a aikace tare da kasar Sin a fannoni daban daban, za kuma ta hada kai wajen kiyaye halaltacciyar moriyar kasashe masu tasowa. (Ibrahim)