Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya ce a matsayin Sin na babbar kasa mai tasowa, da Amurka dake matsayin babbar kasa mai wadata, kamata ya yi su karfafa tattaunawa, tare da kyautata matakan su na shawo kan sabanin dake tsakaninsu yadda ya kamata.
Han Zheng, wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin ganawarsa da jagororin kungiyoyin kawance na Amurka, da kwararru, da sauran mutane daga sassan rayuwa mabanbanta, a gefen taron kolin MDD dake gudana yanzu haka a birnin New York, ya yi kira ga sassan biyu da su nacewa manufofin nan 3 na mutunta juna, da zaman jituwa, da hadin gwiwar cimma moriya tare, wadanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, kana su aiwatar da muhimmiyar yarjejeniyar da shugabannin kasashen 2 suka amincewa, yayin taron Bali na kasar Indonesia. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp